Wasu gungun yan dabar siyasa sun tare motocin jami’an yan sanda da yan jarida a garin Janruwa dake karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano lokacin da suke kan aikinsu na duba yadda zaben cike gurbi yake gudana.
Yan jaridar dai suna cikin masu daukar rahoto a hukumomin tsaron jihar , wadanda motarsu ta lalace, bayan sun bar garin Bagwai don zuwa karamar hukumar Ghari, tare da tawagar hukumomin tsaron wadanda aka barsu a baya.
Daga baya rundunar yan sandan jihar Kano, ta turo wasu motocin yan sanda don su tafi da yan jairdar da motarsu ta lalace, inda akan hanyarsu daidai garin Janruwa dake karamar hukumar Bagwai, gungun yan dabar siyasar suka tare motocin tare hana su wucewa.












