• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yanbindiga sun bukaci Naira biyan daya kudin fansa domin sakin mutane 286

aksam by aksam
March 14, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
472
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Ƴan bindiga da suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikata 286 a wata makaranta a arewacin Nijeriya a makon da ya gabata, sun bukaci a ba su Naira biliyan ɗaya, kwatankwacin dala 620,432 a matsayin kuɗin fansa, kamar yadda kansilan yankin kuma mai magana da yawun iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A ranar 7 ga watan Maris ne aka sace yara ƴan makarantar da ma wasu manyan ɗalibai da kuma wasu ma’aikatan makarantar a garin Kuriga da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Nijeriya, a karon farko da aka yi garkuwa da mutane da dama irin haka tun shekara ta 2021.

RelatedPosts

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Kansilan, Jubril Aminu, wanda kuma shi iyalan wadanda aka yi garkuwa da su suka zaɓa ya dinga magana a madadinsu, ya ce masu garkuwan sun kira shi ta wayar tarho ranar Talata.

“Sun buƙaci a biya su biya jimillar naira biliyan ɗaya a matsayin kudin fansa ga ɗaukacin ɗalibai da ma’aikatan makarantar,” in ji Aminu.

“Sun ba da wa’adin biyan kudin fansa cikin kwanaki 20, daga ranar da aka yi garkuwa da su, sun ce za su kashe dukkan ɗaliban da ma’aikata idan har ba a biya kuɗin fansar ba.”

Shi ma Idris Ibrahim, wani zaɓaɓɓen jami’i a karamar hukumar Kuriga, ya tabbatar da batun bukatar kudin fansa da adadin kudin.

“E, masu garkuwa da mutane sun kira al’ummar ta lambar Jubril Aminu, suka kuma gabatar da bukatar,” in ji shi.

Ibrahim ya shaida wa Reuters cewa, “Sun kira ne daga wata ɓoyayyiyar lamba amma hukumomi na aiki don gano lambar.”

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na daukar ƙwararan matakai domin ganin an sako daliban.

Reuters ya ruwaito cewa Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, bai amsa saƙon da ta aika masa ta son jin ta bakinsa ba game da buƙatar masu garkuwa da mutane.

Haka shi ma mai magana da yawun Shugaba Tinubu bai amsa buƙatar son jin ta bakinsa ba.

Sai dai, Ministan yada labaran kasar, Mohammed Idris, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa, matsayar Tinubu kan sace-sacen da aka yi a Kuriga shi ne jami’an tsaro su tabbatar da sako mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan masu garkuwa da mutanen ba.

“Shugaban kasa ya ba da umarnin cewa dole ne jami’an tsaro cikin gaggawa su tabbatar da cewa an dawo da wadannan yaran da duk wadanda aka yi garkuwa da su lafiya, sannan kuma su tabbatar ba a biya ko sisin kwabo domin kudin fansa ba.”

Gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari ta kafa dokar hana biyan kudin fansa inda ta ce za a ɗaure duk wanda aka samu ya biya kudin fansa don a sako wani nasa.

Share189Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Jam’iyar PDP ta magantu kan dakatar da sanatan da ya bankado cushen kusan tiriliyan hudu da Akpabio yayi

Next Post

Sha’aban Sharada ya rasa matsayinsa bayan da Tinubu ya maye gurbinsa Lawan Jafaru Isa

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano
LABARAI

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

by Abdulhamid Isa
September 7, 2026
Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Yanbindiga sun farmaki masallata yayin da suke tsaka da jam’i a wata jihar Arewa

Yanbindiga sun farmaki masallata yayin da suke tsaka da jam’i a wata jihar Arewa

March 8, 2024
Shugaban kasar Türkiye ya mika daruruwan gidaje ya ya gina wa wadanda girgizar kasa ta shafa

Shugaban kasar Türkiye ya mika daruruwan gidaje ya ya gina wa wadanda girgizar kasa ta shafa

February 6, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

September 7, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Wata Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Watanni Uku Bisa Satar Kayan Mota

Wata Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Watanni Uku Bisa Satar Kayan Mota

August 29, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media