Jaridar Legit ta bayyana cewa A kwanakin baya ne wata kafar yaɗa labarai ta bayyana cewa bincikenta ya gano yadda ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya raba buhunan shinkafa 50 ga wasu zaɓaɓɓun ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Shafin ya yi iƙirarin cewa Matawalle, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya bayar da tallafin ne ta hannun Honorabul Musa Bawa Yankuzo.
Sai dai kafar yaɗa labarai ta Zamfara Newsletter, ta ƙaryata rahoton, tana mai cewa wani ƙoƙari ne na ƴan adawa domin su ɓata sunan tsohon gwamnan.
Kafar yaɗa labaran ta ce Yankuzo, wanda ake zargi da bayar da kayan ga ɗaya daga cikin shugabannin ƴan bindigan da ake nema ruwa a jallo, Ado Aleiro, a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, ya musanta zargin.
Wani na kusa da Yankuzo cikin wata sanarwa da ya aikewa jaridar Legit ya bayyana cewa: “Honorabul Musa Bawa Yankuzo ya bar ƙasar ne a ranar 5 ga watan Maris zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah kuma ana sa ran zai dawo Najeriya a makon farko na watan Mayun 2024.”










