Gwamnatin Bayelsa ta amince za ta fara biyan ma’aikatan kananan hukumomi N80,000 a matsayin mafi karancin albashi
Muƙaddashin gwamnan jihar, Lawrence Ewhrudjakpo ya sanar da haka a taron kwamitin aiwatar da dokar albashi a gidan gwamnati da ke Yenagoa
Ya ce Bayelsa ba ta da ƙarfin tattalin arzikin da za ta bi tsarin gwamnatin tarayya wajen aiwatar da dokar albashin










