Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana takaici kan halin da ‘yan jarida su ka tsinci kansu a ciki.
Atiku Abubakar, wanda yayi takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata a jam’iyyar PDP ya ce ‘yan jarida haske ne ga al’umma.
Kana ya caccaki gwamnatin Tinubu kan karuwar garkuwa da mutane a sakon da ya wallafa a shafinsa na X,
Atiku Abubakar ya ce da takaici matuka yadda gwamnati da ‘yan ta’adda su ke kokarin sako ‘yan jarida a gaba. “An shiga masifar rashin tsaro,”
Atiku Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnati kan yadda ta ke kokarin kama wa tare da garkame ‘yan jarida.
Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da ya ce ‘yan ta’adda sun hana mutanen kasar nan, ciki har da ‘yan jarida a sakat.
Ya bayyana fargabar halin da ‘yan kasa ke ciki bayan sace tsohon shugaban kungiyar ma’aikatan hasken wuta da gas, Takai Shamang mai shekaru 78.
Atiku ya kara da cewa a yan kwanakin nan, an sace Alkaliya Janet Galadima Gimba da yaranta, duk da an sako yaran daga baya, sai kuma mahaifiyar mawaki Rarara









