Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan bullar wata kungiya da ke tallata auren jinsi a jihar.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da samun labarin kungiyar da ake kira ‘WISE’ inda ta ce ta kaddamar da bincike kan lamarin.
Hadimin gwamnan a bangaren sadarwa, Hassan Sani Tukur shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yammacin yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024.
Hassan ya ce gwamnatin ta tabbatar da cewa ba za ta amince da duk wani iya shege makancin haka ba a jihar.











