• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Zai Yi Balaguron Mako Biyu Zuwa Faransa, Kenya Da Ruwanda

aksam by aksam
May 2, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home KETARR
ADVERTISEMENT
465
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

 

Daga: Hassan Umar Gwammaja

RelatedPosts

Shugaban Amurka Trump Da Na Rasha Suna Tattaunawa Yanzu Haka

Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Ziyarci Al’ummomin Da Ambaliya Ta Yi Wa Barna A Kasarsa

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Mista Bayo Onanuga, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare.

Da yake fayyace yadda tafiyar za ta kasance, Onanuga ya ce matakin farko na tafiyar Shugaba Ƙasar zai kasance a ƙasar Faransa, daga nan kuma zai tafi Nairobi ta ƙasar Kenya domin halartar taron “Africa-France Summit” wanda aka tsara zai fara a mako mai zuwa

 

Taron, wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban Kenya William Ruto suke jagoranta tare, zai maida hankali kan sauyin makamashi, bunƙasa masana’antu marasa aiki da fetur, sauyin dijital, sake fasalin tsarin kuɗaɗen duniya, da kuma matakan yaƙi da sauyin yanayi.

 

Onanuga ya ce halartar Shugaba Tinubu a taron daga ranar 11 zuwa 12 ga Mayu zai ƙara jaddada ƙudirin Nijeriya na ƙarfafa haɗin gwiwar dabaru da ƙasashen Afrika da Jamhuriyar Faransa.

Taron mai taken “Africa Forward: Africa-France Partnerships for Innovation and Growth”, zai samar da babban dandali ga shugabannin Afrika da takwarorin su na Faransa domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi nahiyar, ciki har da sauyin tattalin arziki, jure wa sauyin yanayi, bunƙasa ababen more rayuwa, ƙarfafa matasa, cigaban fasaha, da kuma gina zaman lafiya.

 

Bayan kammala taron na Kenya, Tinubu zai tafi Kigali, babban birnin ƙasar Ruwanda, domin halartar taron shekara-shekara na “Africa CEO Forum” wanda za a gudanar daga ranar 14 zuwa 15 ga Mayu.

Taron na bana mai taken “Scale or Fail” shi ne mafi girman taron shugabannin kamfanoni masu zaman kan su na Afrika, masu zuba jari, da masu tsara manufofi, inda za a mai da hankali kan hanzarta sauyin tattalin arziki ta hanyar haɗin kai, haɗa yankuna, da ƙara zuba jari tsakanin ƙasashe.

Ana gudanar da taron ne tare da haɗin gwiwar “International Finance Corporation”, kuma zai haɗa sama da manyan shugabanni 2,000 da jagororin ƙasashe domin tattauna dabarun gina masana’antu masu ƙarfi da gasa.

A dukkanin tarukan biyu, Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabai da za su nuna gyare-gyaren da gwamnatin sa take yi domin mayar da Nijeriya cibiyar da ta dace don zuba jari da bunƙasa tattalin arziki.

Haka kuma, zai yi ganawa da manyan shugabannin kasuwanci na duniya da na Afrika.

Shugaban zai tafi tare da wasu ministoci da manyan mataimakan sa, kuma ana sa ran zai dawo Nijeriya bayan kammala taron Ruwanda.

Share186Tweet116SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Wasu Dalilin Da Suka Sa Kwankwaso Ke Shirin Ficewa Daga Jam’iyyar ADC

Next Post

Tinubu Ya Sanya Dokar-Ta-Baci Kan Yunwa Da Rashin Tsaro a Najeriya

aksam

aksam

RelatedPosts

Shugaban Amurka Trump Da Na Rasha Suna Tattaunawa Yanzu Haka
KETARR

Shugaban Amurka Trump Da Na Rasha Suna Tattaunawa Yanzu Haka

by aksam
March 18, 2025
KETARR

Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Ziyarci Al’ummomin Da Ambaliya Ta Yi Wa Barna A Kasarsa

by aksam
August 10, 2024

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Rahotanni Na Nune  Da Cewar An Tsige Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Kano

Rahotanni Na Nune Da Cewar An Tsige Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Kano

April 2, 2026

Shugaba Tinibu ya bada sabon umarni ga Hukumar Kwastam

March 10, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media