• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Tinubu Ya Sanya Dokar-Ta-Baci Kan Yunwa Da Rashin Tsaro a Najeriya

aksam by aksam
May 2, 2026
Reading Time: 1 min read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Hassan Umar Gwammaja

RelatedPosts

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana matsalar yunwa, fatara da rashin tsaro a matsayin manyan matsalolin da ke bukatar kulawa ta gaggawa, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da za a ɗauki tsauraran matakai domin magance su a faɗin ƙasar nan.

Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, wanda ya wakilce shi a bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya ta 2026 da aka gudanar a Eagle Square da ke Abuja.

A cewarsa, rashin tsaro na hana manoma komawa gonaki yadda ya kamata, lamarin da ke rage yawan amfanin gona tare da ƙara jefa al’umma cikin yunwa da fatara.

Ya ce matsin tattalin arziki da hauhawar farashi sun ƙara tsananta rayuwar ‘yan Najeriya, don haka gwamnati ta ɗauki wannan lamari a matsayin abin da ya dace a ba fifiko cikin gaggawa.

Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa ta fara aiwatar da matakai daban-daban da suka haɗa da ƙarfafa tsaro, rage talauci, da samar da ayyukan yi musamman ga matasa domin rage zaman kashe wando da inganta rayuwar al’umma.

Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnati na shirin samar da guraben aiki ga matasa 45,000 domin taimakawa wajen ƙarfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya a sassa daban-daban na ƙasar.

Tinubu ya ƙara da cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da ƙungiyoyin ma’aikata na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan matsalolin da suka addabi Najeriya.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Zai Yi Balaguron Mako Biyu Zuwa Faransa, Kenya Da Ruwanda

Next Post

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Ya Fice Daga Jam’iyar PDP

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano
LABARAI

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

by Abdulhamid Isa
September 7, 2026
Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Sarki Sanusi ll ya yi martani ga masu ganin sai wanda marigayi Ado Bayero ya haifa ne zai zama sarkin kano

Sarki Sanusi ll ya yi martani ga masu ganin sai wanda marigayi Ado Bayero ya haifa ne zai zama sarkin kano

May 25, 2024
Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Gwamnan Rikon Kwarya A Jihar Riverss

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Gwamnan Rikon Kwarya A Jihar Riverss

March 18, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

September 7, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media