• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Wasu Dalilin Da Suka Sa Kwankwaso Ke Shirin Ficewa Daga Jam’iyyar ADC

aksam by aksam
May 2, 2026
Reading Time: 3 mins read
0
Home SIYASA
ADVERTISEMENT
470
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

 

 

RelatedPosts

Dawo da tallafin man fetur

Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa

Mataimakin shugaban kasa zai jagoranci tawaga zuwa Jamhuriyyar Benin

Daga Hassan Umar Gwammaja

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya na ta shirye-shiryen barin jam’iyyar ADC zuwa jam’iyyar NDC.

Aksam Media ta hadu wasu dalilai daban-daban da ake ganin su ne suke kokarin baiwa Kwankwaso damar ficewa daga jam’iyyar ta ADC da a yanzu haka bai wuce kwanaki 33 da komawa cikinta.

Akwai wasu Rahotanni da ke cewa Kwankwaso na son komawa NDC ne saboda kokarin da aka ce Tsohon shugaban Kasa Obasanjo na yunkurin hada kwankwaso da Peter Obi takarar shugaban Kasa a jam’iyyar a zaɓen 2027.

Amma a wata hira da aka yi da makusancin Kwankwaso Shehu Wada Sagagi ya ce yawan tarin shari’un jam’iyyar ADC dake gaban kotuna ne yasa dole su fice daga jam’iyyar domin gudun matsala bayan zabe.

 

Shehu Wada ya ce Karin Kan wancan dalilin har da bukatar da gwamnatin tarayya ta mikawa INEC na neman a rushe jam’iyyar ta ADC saboda a zaɓen da ya gabata ba ta sami Nasarar lashe zaben ko da na Dan majalisa ba ne.

Ya ce dole ne su nemi mafita domin Kalubalantar jam’iyyar APC wacca ta Kasa kamarwa yan Kasa abubuwan da suke bukata.

Yusuf Kofar mata shi ma wani Babban hadimi ne a gidan kwankwaso shi ma ya bayyana wasu dalilai da ya ce sun ishe su dalilin ficewa daga jam’iyyar ADC.

 

Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC na fuskantar manyan kalubale na cikin gida da na waje da ka iya kawo cikas ga hadin kanta da kuma ci gabanta a matsayin jam’iyyar adawa.

“Duk da hukuncin Kotun Koli da ya yi wa jam’iyyar ADC gata a shari’ar da ta shafi Nafi’u Bala, akwai barazana a ci gaba da daukar hakan a matsayin cikakkiyar nasara. Rahotanni sun nuna cewa Kotun Kolin ta soke umarnin ci gaba da zaman yadda ake ciki ne kawai, yayin da shari’ar asali ke ci gaba a Babbar Kotun Tarayya, lamarin da ke haifar da fargaba kan abin da zai biyo baya”.

 

Haka zalika, Kofarmata ya ce kwanan nan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke zabukan cikin gida da kuma babban taron jam’iyyar na kasa, matakin da ke kara jefa jam’iyyar cikin wani sabon rudani na shari’a wanda ke bukatar daukar matakin gaggawa.

“A jihar Kano ma, wani bangare na jam’iyyar ya shigar da kara a Babbar Kotun Jiha, inda kotun ta dage sauraron shari’ar na tsawon wata guda. Bugu da kari, bangaren ya sake shigar da wata kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, yana neman a dakatar da shugabannin jam’iyyar na jiha daga gudanar da duk wani aiki, ciki har da zaben fidda gwani, inda ake sa ran fara sauraron karar nan ba da jimawa ba”. Inji Yusuf Kofarmata

Ya kara da cewa A gefe guda kuma, an rawaito cewa shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ya gargadi jam’iyyar ADC da ta yi taka-tsantsan domin kaucewa irin abin da ya faru da jam’iyyar APC a jihar Zamfara a shekarar 2019, lokacin da ta rasa dukkan kujerunta sakamakon hukuncin kotu. Sai dai wasu na ganin wannan gargadi na iya kara dagula al’amura maimakon rage su.

Kofar mata ya ce ana zargin gwamnatin APC karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu da hannu wajen haddasa yawancin rikice-rikicen da ke addabar jam’iyyun adawa, zargin da ke kara jawo cece-kuce a fagen siyasa.

Dangane da haka, masu sharhi na kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su yi zurfin tunani kan wadannan matsaloli tare da nemo mafita mai dorewa domin tabbatar da cewa jam’iyyar ADC ta samu damar shiga zaben shekarar 2027 ba tare da tangarda ba.

Baya ga wadannan dalilai da Kofar mata ya bayan, Muna daf da kammala hada Wannan rahoton Jaridar Aksam Media ta ci karo da wani rahoto na Jaridar The Cable da ke cewa Kwankwaso da Peter Obi za su koma jam’iyyar NDC a mako mai zuwa.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar Kwankwasiyya Habibu Sale mailemo ya fitar .

Share188Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

INEC Ta Sanya Ranar Zaben Cike Gurbi Na Kujerar ‘Yan majalisar Tarayya A Kano Da Sasu Jihohi

Next Post

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Zai Yi Balaguron Mako Biyu Zuwa Faransa, Kenya Da Ruwanda

aksam

aksam

RelatedPosts

Atiku Ya Nemi Tinibu Ya Fadi Inda Ya Saka Tiriliyan 30 na Tallafi Mai Da Ya Cire.
SIYASA

Dawo da tallafin man fetur

by Khadija Maitaya
August 26, 2026
Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa
SIYASA

Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa

by Khadija Maitaya
July 28, 2026
Mataimakin shugaban kasa zai jagoranci tawaga zuwa Jamhuriyyar Benin
SIYASA

Mataimakin shugaban kasa zai jagoranci tawaga zuwa Jamhuriyyar Benin

by Khadija Maitaya
July 23, 2026
Daukar DanKwankwaso Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano A NDC Ya Jaho Ce-ce-ku-ce
SIYASA

Daukar DanKwankwaso Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano A NDC Ya Jaho Ce-ce-ku-ce

by aksam
June 16, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Yadda aka Gano Ramin Karkashin Kasa da Masu Garkuwa Suke tara mutane

Yadda aka Gano Ramin Karkashin Kasa da Masu Garkuwa Suke tara mutane

January 25, 2024

De evolutie van online kansspelen: kansen, regelgeving en technologische innovatie

April 21, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media