Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026 domin gudanar da zabukan cike gurbi a kujerun majalisu da suka zama babu kowa a kai a jihohi shida na kasar nan da suka hada da, Kebbi, Kano, Ondo, Rivers, Nasarawa da Enugu.
A cewar hukumar, kujerun Sanatoci guda hudu ne za a cike, wadanda suka hada da:
Jihar Ondo (bayan murabus din Sanata Jimoh Ibrahim wanda aka nada a matsayin wakilin dindindin na Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya)
Jihar Rivers (bayan rasuwar Sanata Barinada Mpigi)
Jihar Nasarawa (bayan rasuwar Sanata Godiya Akwashika)
Jihar Enugu (bayan rasuwar Sanata Okey Ezea)
Haka kuma, za a gudanar da zaben cike gurbi na kujera guda daya ta Majalisar Wakilai a Jihar Kano, da kuma kujera guda daya ta Majalisar Dokokin Jihar Kebbi.
INEC ta bayyana cewa za a gudanar da wadannan zabuka ne a rana guda da zaben gwamnan Jihar Ekiti da aka shirya yi a ranar 20 ga Yuni, 2026.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana jadawalin zaben yayin rantsar da sabuwar Kwamishinar Kasa, Rear Admiral Jamila Malafa (mai ritaya).












