Hassan Umar Gwammaja
Mai taimaka masa na musamman (PPS), Mustapha Abdullahi Junaid, wanda ya tabbatar da mutuwarsa a shafinsa na sada zumunta.
Inda ya rubuta cewa: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Da bakin ciki nake sanar da rasuwar ubanmu mai daraja, Alhaji Aminu Alhassan Dantata. Allah ya jikansa da rahama ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, ya gafarta masa kura-kuransa. Za a sanar da cikakkun bayanai kan jana’iza daga baya insha Allah.”
Allah ya jikan shi da rahamarSa, ya kuma ba iyalansa hakurin jure wannan rashi.












