Rundunar ‘yan Sanda ta kasa reshen jihar Delta ta yi kira ga wadanda ake cin zarafin su a gidajen aure, musamman mata su kai kara a ofishin ‘yan Sanda mafi kusa a maimakon yin korafi a dandalin sada zumunta.
Kakakin rundunar ‘Yan Sanda na Jihar Delta SP Bright Edafe ne ya bada wannan shawarar a kafar sada zumunta ta X da yake maida martani a kan hoton wata mace da aka kafa a dandalin sada zumunta na rundunar ‘Yan sandar jihar Delta, na wata mace da fuskarta a kumbure da bandeji jina-jina da aka ce maigidanta ne ya lakada mata duka, kuma ‘yan sanda basu dauki wani mataki ba.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Delta ya maida martani a shafinsa na X cewa,
“Kina auren wani mutum a Asaba yana dukanki kullum, kina da ‘yan uwa, kina da abokai; kuma kuna da ofisoshin ‘yan sanda sama da shida a Asaba. Kun ki kai karar shi, amma kun gwammace ku zo kan dandalin sada zumunta X don ku yi kuka ga ’yan sanda su zo su taimaka.”
Kakakin rundunar “yan sandan ya shawarci mata su rika zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su, domin kai rahoto, kada su saurari abokansu da zasu kashe masu guiwa da cewa, “Wannan Najeriya ce”. Ya ce babu abinda ya alakanta Najeriya da rashin kai rahoto ofishin ‘yan sanda.













Comments 1