DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
shugabannin jam’iyyar a matakin mazaba suka bulla, inda suka sake sanar da dakatar da mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Umar Ganduje.
Majiyarmu ta ruwaito cewa sabon tsagin shugabancin jam’iyyar a mazabar Ganduje cikin karamar hukumar Dawakin Tofa sun ce su ne halastattun shugabannin jam’iyyar daaka zaba a 31 ga watan Juli, 2021.
Da ya ke ganawa da manema labarai a Kano, Sakataren jam’iyyar na mazabar Ganduje Ja’afar Adamu, da ya yi magana a madadin sauran shugabannin jam’iyyar 11, ya ce dakatar da Ganduje a jam’iyyar ya zama wajibi biyo bayan zarginsa da yin ‘Anti Party’ wato yi wa jam’iyya zagon kasa musamman a zaben da ya gabata da ba ta yi nasara ba.
Ja’afar Adamu wanda dan’uwa ne na jini ga tsohon Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje, ya zargi mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa da kitsa wutar rikici da ta yi sanadiyar tabarbarewar lamurran jam’iyyar da yawa.











