Daga: Hassan Umar Gwammaja
Majalisar koli ta addinin musulunci a Najeriya (NSCIA) ta bukaci Musulmi a fadin Najeriya da su fara duban jinjirin watan Ramadan 1447 A.H. bayan faduwar rana a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga Sha’aban 1447 A.H.
A sanarwar da babban sakataren majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede ya sanya wa hannu, an ce kwamitin duban wata na kasa tare da hadin gwiwar hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya (NASRDA) za su kula da aikin tabbatar da ganin watan.
Majalisar ta bayyana cewa idan an ga jinjirin watan a daren Talata, Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar, Muhammad Sa’ad Abubakar, zai sanar da Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026 a matsayin ranar farko ta azumin Ramadan. Idan kuwa ba a ga watan ba, Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026 za ta zama ranar farko ta azumin.












