• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Mafi karancin albashi, NLC ta nemi gwamnan Gombe ya yi murabus

aksam by aksam
August 5, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
465
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta buƙaci Gwamnonin da ba su iya biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da su sauka daga mukamansu.

Hakan na zuwa ne a matsayin martani ga Gwamnan Jihar Gombe Inuwa Yahaya wanda a kwanakin baya ya bayyana cewa Gwamnatin sa ba za ta iya biyan sabon mafi ƙarancin albashin Ma’aikata na kasa ba.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Gwamna Yahaya wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Arewa ya bayyana haka a lokacin wata ganawa da shugabannin kungiyoyin kwadago da kungiyoyin ‘yan kasuwa a gidan Gwamnati da ke Gombe.

A tsokacin da Gwamna Yahaya ya yi, Benson Upah Shugaban hulɗa da jama’a na NLC ya shawarci Gwamnan da ya yi murabus.

“Ya yi murabus idan ba zai iya biya ba, ya yi rantsuwar aiki don tabbatar da doka kuma ba zai karya ta ba,” in ji Upah.

Kun tuna cewa a makon da ya gabata ne Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar mafi karancin albashi a hukumance ta maida mafi karancin albashin Ma’aikata zuwa Naira 70,000 daga Naira 30,000.

Wannan matsayar ta biyo bayan tattaunawar kusan makonni biyu da Shugaban ƙasar ya yi da kungiyoyin kwadago wadanda tun farko suka bukaci a biya su Naira 250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

A ranar 18 ga watan Yuli ne Gwamnatin Tarayya, da kungiyoyin kwadago da masu zaman kansu suka kammala tattaunawa na tsawon watanni da suka kwashe suna tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin Ma’aikata wanda hakan ya sa aka cimma matsaya kan adadin Naira 70,000 a kowane wata.

Daga bisani a ranar 15 ga watan Yuli Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta dora wa Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare nauyin shiryawa da gyara kudiri na gyara kasafin kudin 2024.

Mako guda kenan Shugaba Tinubu ya miƙa bukatar Majalisar dattawa ta gyara dokar kasafi ta 2024 da kuma dokar kudi ta 2023 inda ya bada shawarar a kara kasafin kudi da Naira Tiriliyan 6.

An aika wasikar ne zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa kuma aka karanta shi a yayin zaman Majalisar.

Share186Tweet116SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Fassarar kalaman shugaban kasa

Next Post

Yadda masana da manyan yansiyasa suka caccaki shugaba Tinubu

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Amurka na shirin Amfani da GBU-57A/B Bom domin ruguza Makamashin nukiliya na Iran

Amurka na shirin Amfani da GBU-57A/B Bom domin ruguza Makamashin nukiliya na Iran

June 19, 2025
Hukumar Bayar Da Agajin Gaggauwa Ta Najeriya NEMA, Tace Adadin Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Rasa Rayukan Su A  Jahohi Goma 15 Na Najeriya Ya Kai 179

Fulani na kokawa da kin damawa da su a gwamnatin Jigawa, kalli dalilin su

September 26, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media