• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yadda masana da manyan yansiyasa suka caccaki shugaba Tinubu

aksam by aksam
August 5, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Fitattun masana da yansiyasa irin su tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, da Gwarzon kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, da Lauya mai kare hakkin ɗan Adam, Femi Falana (SAN) da wasu kungiyoyin farar hula (CSOs) sun caccaki Jawaban da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ga ƴan Najeriya inda suka ce bai yi magana kan muhimman batutuwan da suka shafi ƙasar ba waɗanda suka janyo zanga-zangar neman kawo ƙarshen Mulkin rashin adalci.

Masu Zanga-zangar da ta fara a ranar Alhamis kuma ta yi sanadin salwantar rayuka mutane da dama tare da lalata kadarori na Biliyoyin Nairori.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Hakan ya sa aka yi kira daga bangarori daban-daban ga Shugaba Tinubu da ya yi wa ƴan Najeriya jawabi domin kawar da damuwar da masu zanga-zangar da sauran ƴan ƙasar suka nuna ciki har da tsadar rayuwa da rashin tsaro a Kasar.

Shugaban ya yi kunnen uwar shegu inda daga bisani ya yi Jawabi a jiya Lahadi yana mai bayyana dalilan cire tallafin Man Fetur da kuma matsayar Naira, inda ya ce waɗannan na daga cikin sauye-sauyen da ya kamata a yi domin ci gaban Najeriya.

Tinubu ya kuma zayyana wasu daga cikin matakan da Gwamnatin sa ta ɗauka domin daƙile illolin waɗannan manufofin, yana mai cewa ‘yan Najeriya za su ci gajiyar hakan a nan gaba.

Sai dai jim kaɗan bayan jawabin, masu sharhi da sauran masu lura da al’amura sun ce jawabin Shugaban ba shi da wani amfani, yayin da masu zanga-zangar suka ce bai nuna wata alama da ke nuna cewa yana sane da ainafin matsalolin da kasar ke fuskanta ba,
Sun ce baya ga rashin yin magana mai Ma’ana kan batun dawo da tallafin Man Fetur da darajar Naira, jawabin nasa mai sakin layi 38 bai ce komai ba kan muhimmin batu wato – rashin tsaro – musamman a Arewacin Najeriya inda aka kori Miliyoyin manoma daga gonakinsu da gidaje.

Zanga-zangar da ake ci gaba da yi ta kara ɗaukar sabon salo a Arewa, inda masu zanga-zangar suka yi zanga-zanga a Kano, da Katsina, da Jigawa, da Sokoto, da Kebbi, da Zamfara, da Kaduna, da Yobe, da Borno, da Nasarawa, da Plateau, da Adamawa da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja suna baje kolin alluna masu dauke da sakonnin da ke nuna bukatar magance yunwa da rashin tsaro. An kuma gudanar da zanga-zangar a yankin Kudu maso Yamma in ban da Jihar Ekiti; wato Kudu maso Kudu, amma mutanen Kudu maso Gabas ba su fito zañga-zañgãr ba.

Da yawa daga cikin waɗanda aka zanta da su a yayin zanga-zangar a wasu Jihohin Arewa kamar Katsina Zamfara da Sokoto sun ce duk da cewa su manoma ne, amma an mayar da su mabarata domin ba su da damar shiga gonakinsu a yanzu saboda ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane sun addabi yankin.

A martanin da ya mayar kan matakin da Tinubu ya ɗauka kan zanga-zangar, Wale Soyinka a wata sanarwa da ya fitar a jiya ya bayyana damuwarsa kan yadda Shugaban ya yi watsi tare da bada damar harbi da kashe masu zanga-zangar da ke neman a samar da Shugabanci na gari.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Mafi karancin albashi, NLC ta nemi gwamnan Gombe ya yi murabus

Next Post

Wani sanata ya fadi gaskiyar abin da yake damun Arewa da kuma yadda za’a iya gyara matsalar

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Ƴan sanda sun ƙwato yarinya ƴar shekara 12 da aka Daura wa aure da mai sheka 63

Ƴan sanda sun ƙwato yarinya ƴar shekara 12 da aka Daura wa aure da mai sheka 63

April 2, 2024

Innovare nella Certificazione dei Processi Agricoli: La Nuova Frontiera della Trasparenza

April 21, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media