• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kwamishinan Harkokin Sufuri na Kano Ya Ajiye Aiki Saboda Cece-kucen Zargin karbar Belin Wanda Ake Zargi da Dillancin Miyagun Kwayoyi

aksam by aksam
August 6, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

Daga Hassan Umar Gwammaja

Kwamishinan Harkokin Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye mukaminsa da yammacin Laraba, bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa don gano rawar da ya taka a belin wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.

‎‎Wannan sau yi ana kallonsa a matsayin wani babban mataki wajen ƙarfafa ɗabi’un gaskiya, da rikon amana a wannan gwamnati.

‎‎A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Kwamishina Namadi ya bayyana cewa murabus ɗinsa na da nasaba da bukatar kare muradun al’umma da kuma la’akari da mahimmancin batun.‎‎

Ya ce: “A matsayina na ɗan gwamnati da ke gaba da gaba wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi, dole ne in ɗauki wannan mataki — kodayake yana da ɗaci. Duk da cewar ina da yakinin ba ni da laifi, ba zan iya watsi da tasirin yadda jama’a ke kallon lamarin ba, da kuma buƙatar kare ƙimar da muka gina tare.

”‎‎‎‎Alhaji Namadi ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na yin hidima wa jiharsa, tare da sake jaddada jajircewarsa wajen gudanar da shugabanci na gari da rikon amana.‎‎

Ya ƙara da cewa:“A matsayina na nagartaccen ɗan ƙasa, dole ne in tsaya tsayin daka wajen kare amana da hangen nesa da muka gina a jihar nan. Zan ci gaba da kasancewa cikin masu biyayya ga akidar da ta kawo wannan gwamnati kan mulki.

”‎‎‎‎A nasa bangaran Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin cikin girmamawa, tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba. Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta sassauta ba wajen yaƙi da laifukan da suka shafi kwayoyi da sauran ɗabi’un banza da ke lalata rayuwar matasa da al’umma gaba ɗaya.‎‎

Gwamnan ya kuma shawarci dukkan masu rike da mukaman siyasa da su rika taka-tsantsan a kan duk wani lamari da ya shafi jama’a, tare da neman izini daga hukumomin da suka dace kafin su tsoma kansu cikin irin waɗannan batutuwa.‎‎

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

An Yi Mummunar Faɗuwa a Sakamakon Jarrabawar Bana – WAEC

Next Post

Gwamnatin Kano Ta Gargadi Jami’anta Dasu Guji Tsoma Baki Kan Abinda Bai Shafe Su Ba A Wani Yunkuri Na Tallafawa Gwamnati Sauke Hakkokin Al’umma

aksam

aksam

RelatedPosts

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi  Annabi Muhammadu SWA  A Garin Nkawkawo
Uncategorized

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

by aksam
September 1, 2026
Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka
Uncategorized

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

by aksam
August 26, 2026
Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano
Uncategorized

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

by aksam
August 26, 2026
Gwajin DNA: Kashi 23.6% Na Gwaje-Gwajen Uba A Najeriya Sun Nuna Rashin Daidaito
Uncategorized

Gwajin DNA: Kashi 23.6% Na Gwaje-Gwajen Uba A Najeriya Sun Nuna Rashin Daidaito

by aksam
August 25, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

The Role of RNGs in Crazystar Games

April 21, 2025
Bayan neman ya yi murabus, Tinubu yace har yanzu Atiku bai gama warkewa ba

Bayan neman ya yi murabus, Tinubu yace har yanzu Atiku bai gama warkewa ba

January 31, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media