Kungiyar matuka manyan motocin haya ta yantanki ta jihar Kano ta jiddada Kudirinta na hada hannu da sabon kwamishinan harkokin sufuri na jihar Kano domin bunkasa harkokin sufuri gaba a fadin jihar Kano.
Shugaban Kungiyar na kasa reshen jihar Kano Kwamared Abdulsalam
Salisu rimin gado ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Manema labarai a ofishinsa dake nan jihar Kano.
Kwamared Abdulsalam salisu yace Kungiyar yantanka ta jihar Kano ta dade tana mu’amulla da kwamishinan harkokin sufuri Alh daderi tun yana matsayin kwamishinan harkokin Shari”a ba Kuma bakon Kungiyar bane saboda da yawan mu’amullar da suka yi a baya.
Shugaban Kungiyar yace saboda da haka Kungiyar matuka manyan motocin ta yantanka za ta tallafawa shugabancin kwamishinan domin ciyar da alummar da sufuri na jihar Kano gaba.
Shugaban ya bukaci hukumomin dake lura da harkokin sufuri na jihar da kwamishina da su sanya Kungiyar matuka manyan motocin tanka ta jihar Kano sakamakon gudunmawar da suke baiwa musamman wajen samarwa matasa ayyukan yi domin dakile shaye shayen muggwan kwayoyi da kwacen wayoyin alumma.
Yace Kungiyar yantanka tana taimakawa Gwamnatin jihar Kano ta fannoni da dama Musamman wajen tattarawa Gwamnatin kudaden haraji wadanda da su ne Gwamnatin take yiwa al’ummar jihar Kano ayyukan ci gaba da kowa zai amfana jihar Kano.
Haka zalika Shugaban Kungiyar yayi Kira ga dukkannin ‘ya’yan Kungiyarsa da su kwantar da hankalunsu domin ma’aikatar sufuri karkashin jagaranci Alh haruna isah dederi Wanda Kungiyar matuka manyan motocin tanka tana yi masa kyakyawan zato zai taimakawa jama’a musamman kungiyin da suke harkokin sufuri na jihar Kano.
Daga karshe Shugaban Kungiyar yayi Kira ga kwamishinan daya fito da kyakyawan tsarin tallafawa kungiyoyi na direbobin matuka motocin haya tun daga Kananan har manya Yadda za su samu damar dogara da kawunansu.












