Kungiyar Yan jaridu na Yanar Gizo Sun Horas da mambabin kungiyar Kan yadda zasu gudanar da aiki a yayin zabe
Shugaban kungiyar yan’jaridun yanar gizon komared Abubakar Abdulkhadir Dangambo yace kungiyar taga dacewar shirya bita ta wuni gida ga ‘ya’yanta hadin gwiwa da gidauniyar Aminu magashi Garba (AGM)
Kwamared Dangamba ya bayyana cewa irin wannan taron bita Yana taimaka wa wajen gogewar ma,aikata a matakai daban daban ta yadda zasu Yi aiki bisa kwarewa
Tsohon shugaban kungiyar yan’jaridun kwamred Abbas Ibrahim shine ya gabatar da bitar da ta kunshi yadda rahoton zai kasance kafin da Kuma bayan zaben hadi da yadda za,a kyaucewa hadarin bata garin dake barazana da rayuwar mutane a lokutan zaben.
Da yake jawabi tsohon famanet sakatare a maaikatar yada labarai ta jihar Kano kwamared Usman Bello ya ja hankalin Yan,jaridun da su kiyaye a lokutan zaben ta hanyar bin ka,idadin da aka koyar dasu domin samun nasara a aikinsu.
Taron ya samu hatattar shugabannin sassan yan’jaridu da suka hadar kungiyar yan’jaridu mata kwamared Bahijja malam kabara da shugaban kungiyar yan’jaridu ta jihar Kano kwamared Sulaiman Abdullahi dederi ,da shugaban jaridar solacebase Abdullatef Abubakar jos da barista Nura kanet da sauran mahimman mutane.
Wakiliyarmu Jamila sulaiman Aliyu ta shaida mana cewa taron ya gudana ne a sakatariyar Yan jaridun Kuma ya samu halattar dimbin Yan jaridun yanar gizon










