Kungiyar masu hada hadar Shanu da dabbobi ta Kasa ta sha Alwashin ci gaba da tallafawa marayun da ‘Ya’yan Kungiyar suka rasu suka bari.
Shugaban Kungiyar Alh Mustapha Ali ne ya bayyana haka a lokacin da Kungiyar take rabawa Marayun Kayayyakin abinci da na Karamar Sallah Wanda ya gudana a nan jihar Kano.
Mustapha Ali yace, Kungiyar tana gudanar da irin wannan tallafin ne,domin taimakawa Marayun Kungiyar don su ji dadin gudanar da rayuwarsu kamar kowa ta hanyar nuna farin cikinsu musamman a lokacin bukukuwan karamar Sallah dake tafe.
Shugaban Kungiyar ya kuma ce,Kungiyar masu safarar Shanu da dabbobi ta tallafawa masu karamin karfi na wannan Kungiya da kudaden da za su yi cefane gabannin Sallar dake karatowa.
Mustapha Ali ya bukaci Shugabanni da Gwamnatoci a matakai daban daban da su kasance masu tallafawa’ya’ya Kungiyoyi masu zaman Kansu da aka mutu ka bar su,kasancewar suna taka mahimmiyar rawa a lokacin da suke raye.
Shugaban ya bayyana cewa, za su ci gaba da taimakawa irin wadan nan marayu dominance su ji dadin gudanar da rayuwarsu kamar kowa.
Daga karshe yayi kira ga sauran’ya’yan Kungiyar da su kara jajircewa wajen baiwa Kungiyar cikakken hadin kai da goyan bayan da ya kamata don ganin Kungiyar ta kara bunkasa harkokin a dukkannin shiyoyinta dake fadin kasar nan.
Ibrahim sani gama












