Gwamnonin jam’iyyar PDP a Najeriya sun fara yunƙurin lalubo hanyar tsamo mutane daga kangin tsadar rayuwa da yunwa
A jiya Litinin, 12 ga watan Fabrairu, 2024 gwamnini suka haɗu a birnin tarayya Abuja domin tattauna halin da ƙasar nan ke ciki
Bayanai sun nuna cewa akalla gwamnoni 6 ne suka halarci zaman wanda ya gudana a masaukin gwamnan jihar Oyo da ke Asokoro
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, wannan taro na gudana yanzu haka a masaukin gwamnan jihar Oyo da ke Anguwar Asokoro a babban birnin tarayya.
Gwamnonin da suka halarci wannan taro sun haɗa da, Bala Mohammed na Bauchi, Seyi Makinde na Oyo, Godwin Obaseki Edo, da Agbu Kefas na jihar Taraba.
Sauran sun haɗa da Dauda Lawal na Zamfara, Caleb Mutfwang na Filato da kuma mataimakan gwamnonin Enugu da Delta, Ifeanyi Ossai da Monday John Onyeme
. Gwamnonin za su duba halin da kasar ke ciki da nufin ba da shawarwarin da za su zamo mafita ga Gwamnatin Tarayya.
Haka nan an ruwaito cewa gwamnonin za su kuma duba matsalar rashin tsaron ƙasar nan da halin da jam’iyyar PDP ke ciki a jihar Edo gabanin zaben gwamna mai zuwa a jihar.













Ni inaganin kamatayayi susa annun jari akayan masarufi yazama mutane suna samun sassauci wajan suya wannan shine hanyar da za aragewa yan gasa radadikawai