Shugabancin kungiyar kasuwar masu sana’ar siyar da magunguna ta kasa reshen jihar kano, ya sha alwashin kawo karshen siyar da magungunan da wa,adinsu ya kare da magungunan da suke sanya maye domin dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi a fadin jihar kano.
Shugaban kungiyar kasuwar Mohammed Musubahu yahaya ne ya jaddada hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake malam kato a nan jihar kano.
Yace, kungiyar ta bijiro da kwamati da yake bibiyar yankasuwa da suke shigo da magungunan marasa inganci da wadanda suke shigo da miyagun kwayoyi domin siyarwa alumma Wanda hakan ba karamar Marsala bace,ga alummar jihar kano, musamman matasa wadanda sune Shugabannin gobe.
Yace,wannan shine kodirin farko da kungiyar ta sanya a gaba saboda gagarumar matsalar take haifarwa a rayuwar alumma.
Mohammed musubahu ya bayyana cewa, baya da haka, Kungiyar za ta hada kai da Gwamnati jihar kano, domin Samarwa ‘ya’yenta tallafin jari da za su bunkasa harkokin kasuwancinsu,musamman duba da kyakyawar Alakar da take tsakanin kungiyar kasuwar da Gwamnatin jihar kano, kasancewar kungiyar ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa Gwamnatin saboda da dannesu da tsohuwar Gwamnatin da ta gabata.
Shugaban yace, kungiyar kasuwar a shirye take wajen baiwa Gwamnati cikakken goyan bayan da suka kamata domin inganta kasuwancin alummar jihar kano.
Ya kuma nuna rashin jin dadinsa bisa,yadda wasu daga cikin yankasuwar suke Neman sanya kananan yankasuwa su tashi zuwa kasuwar Dangwauro don ci gaba da kasuwaci a cen,inda ya bayyana cewa, Wanda gurin yayi mutukar yiwa yankaswar tsada idon aka kwatanta da rukunin kasuwar da suke yanzu, wato,Karami Plaza.
Ya bayyana cewa, yanzu haka, yankasuwa suna biyan kudade naira dubu Dari uku a kowanne shago duk shekara,kuma, masu rukunin kasuwar sun samarwa alumma jami’an tsaro da ruwa da wutar lantarki domin gudanar da kasuwacinsu yadda ya kamata.
Mohammed yahaya yace,kasuwar Dangwauro tayi mutukar yiwa yankasuwa tsada su biya har sama da miliyan daya kudin haya a shekara, baya ga kuma, Nisan da take da shi.
A don haka, Wannan sabon shugabancin kungiyar kasuwar da ya zo,yake ta fafutukar samarwa ‘ya’yanta mafita akan kasuwancinsu,musamman uwar kungiyar kasuwar da ke Babban birnin tarayya Abuja,Wanda yanzu haka, itace,ta dauki dawainiyar ragamar shariar da kungiyar kasuwar take yi akan komawa kasuwar ta Dangwauro dake Naibawa a nan jihar kano.
Uwar Kungiyar tace,wannan sabon shugabancin ya zo managartan tsare_tsare da za su bunkasa harkokin kasuwancin alummar jihar kano da kakkabe maragurbin mutane a harkar kasuwancin magani duba da dimbin alummar dake cin Abinci da sana,ar musamman ma matasa wadanda yanzu sune suka fi yawa a kasuwancin.
Shugaban kungiyar kasuwar yace,sai dai babban abun da shugabancin kungiyar yake bukata bai wuce hadin kan yankungiyar ba,saboda sai da hadin kan yankungiyar ne,za ta samu damar bijiro da ayyuka da za su bunkasa harkokin kasuwancin jama’ar dake sana’ar a fadin jihar kano da ma kasa baki daya.
Haka zalika ya jaddada cewa, duk wani da zai kawo koma baya ko nakasu kungiyar kasuwar ba za ta gajiya ba wajen dakatar da shi daga yunkurinsa na lalata sana’ar,saboda zai yiyu wasu tsirarin mutane su dannewa wasu hakkokinsu ba.
Daga karshe ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda Gwamnatin jihar kano take baiwa kungiyar goyan bayan da suka kamata domin sauke Nauyin da Allah ya Dora mata a matsayin Uwar kowa a fadin jihar kano.
Ibrahim sani gama











