• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kudirin E-Health: Yadda Sanata Barau, “Sanatan Fasahar Zamani”, Ke Jagorantar Makomar Fasahar Kiwon Lafiya A Nijeriya

aksam by aksam
July 12, 2026
Reading Time: 4 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

 

Daga Hassan Umar Gwammaja

RelatedPosts

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

Sai shugabanni masu hangen nesa da gogewa a matakin duniya ne za su fahimci muhimmanci da buƙatar samar da cikakken tsarin doka da zai jagoranci amfani da fasahar zamani a harkar kiwon lafiya.

Wannan ne ya sa kudirin Dokar eHealth na Ƙasa na shekarar 2026, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, CFR, PhD, ya gabatar a zauren Majalisar Dattawa makonnin da suka gabata, ya zama wata babbar shaida ta hangen nesansa wajen daidaita tsarin kiwon lafiyar Nijeriya da yadda ake gudanar da shi a ƙasashen duniya.

 

Bayan da kudirin ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa kwanaki uku da suka gabata, hakan ya ƙara tabbatar da cewa Majalisar Dattawan Nijeriya na da ‘yan majalisa masu zurfin tunani da fahimtar yadda ake tafiyar da harkoki a ƙasashe masu ci gaba, musamman a fannin kiwon lafiya.

 

Lokacin da yake bayyana muhimmancin kudirin a zauren Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin ya ce duniya ta shiga wani sabon zamani inda fasahar zamani ta zama ginshiƙi wajen inganta ayyukan kiwon lafiya.

 

A cewarsa, ƙasashe masu ci gaba da ma waɗanda ke tasowa na amfani da bayanan marasa lafiya a kimiyince, likitanci ta intanet (Telemedicine), basirar wucin gadi (Artificial Intelligence), manhajojin lafiya na wayar hannu da sauran fasahohi domin sauƙaƙa samun kulawar lafiya, rage kuɗin jinya da kuma inganta sakamakon magani.

 

Ya ce Nijeriya ba za ta ci gaba da zama a baya ba yayin da sauran ƙasashen duniya ke cin gajiyar wannan sauyi. Bayan gabatar da kudirin, ‘yan Majalisar Dattawa sun amince da shi baki ɗaya, inda aka miƙa shi ga Kwamitin Lafiya na Majalisar Dattawa domin ci gaba da nazari kafin ya dawo zauren Majalisar. An ba kwamitin sati biyu da ya dawo da kudurin bayan ya duba.

 

Sanata Jibrin ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da aka yi tsawon shekaru wajen inganta fannin lafiya, har yanzu ana fuskantar matsaloli masu yawa. Ya ce yawancin asibitoci na ci gaba da adana bayanan marasa lafiya a takarda, abin da ke haddasa ɓacewar bayanai, jinkirin magani, maimaita gwaje-gwaje da kuma kura-kuran da za a iya kauce wa.

 

Wannan bayani, ya nuna cewa Sanatan yana da cikakkiyar fahimta game da yadda duniya ke tafiya wajen amfani da fasahar zamani domin bunƙasa tsarin kiwon lafiya.

 

A matsayinsa na gogaggen shugaba, ɗan majalisa mai hangen nesa da kuma mai bincike, ya yi bayani dalla-dalla kan dalilan da suka sa tsarin kiwon lafiya na fasahar zamani ya zama wajibi ga kowace ƙasa da ke son inganta kula da lafiyar al’ummarta.

 

Ya ce Nijeriya ba za ta iya ci gaba da zama a baya ba yayin da sauran ƙasashe ke rungumar wannan sauyi. Duk da irin jarin da gwamnati ta zuba a fannin lafiya tsawon shekaru, har yanzu akwai manyan matsaloli da ke addabar tsarin.

Kamar yadda cibiyoyin lafiya da dama ba sa musayar bayanan marasa lafiya cikin aminci, wanda hakan ke rage ingancin ayyukan lafiya.

 

Saboda kusancinsa da al’umma, ya tuna da halin da miliyoyin ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman waɗanda ke zaune a yankunan karkara da wuraren da ke da wahalar isa. Ya ce waɗannan mutane na ci gaba da fuskantar ƙalubalen samun ƙwararrun likitoci saboda ƙarancin ma’aikatan lafiya da kuma nisan wuraren da suke zaune.

 

A matsayinsa na mai digirin digirgir (PhD), ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar samar da doka mai ƙarfi da za ta tsara yadda za a gudanar da ayyukan kiwon lafiya na dijital domin tabbatar da inganci da daidaito.

 

Ya tunatar da Majalisar cewa annobar COVID-19 ta tabbatar da cewa fasahar kiwon lafiya ba wani zaɓi ba ce kawai, illa muhimmin ginshiƙi ne wajen tabbatar da ci gaba da ba da ayyuka na lafiya. Musamman ta hanyar amfani da likitanci ta intanet da tsarin musayar bayanan lafiya na musamman ba tare da buƙatar cudanya kai tsaye ba.

 

Wajen da ya kara burge ni shine lokacin da ya kuma yi gargadin cewa idan babu cikakkiyar doka da za ta jagoranci wannan tsari, za a ci gaba da fuskantar matsalolin aiwatarwa, rashin daidaiton ƙa’idoji, gazawar tsarin musayar bayanai tsakanin cibiyoyi, raunin shugabanci da kuma rashin fayyace nauyin da ke kan masu ba da ayyuka na lafiya ta hanyar dijital.

 

Har ila yau, ya jaddada muhimmancin kare sirrin bayanan marasa lafiya. Ya ce bayanan lafiya na daga cikin bayanan sirri mafi muhimmanci, saboda haka kudirin ya tanadi matakai masu ƙarfi domin kare sirri, inganci da tsaron bayanan marasa lafiya.

 

Sanatan ya kuma bayyana cewa kudirin ya yi daidai da manufofin Gwamnatin Tarayya na sauya harkokin gwamnati zuwa tsarin yanar gizo, Tsarin Bunƙasa Kiwon Lafiya na yanar gizo na Ƙasa, Dokar Lafiya ta Ƙasa, manufar Samar da Kiwon Lafiya Ga Kowa, Dokar Kare Bayanai ta Nijeriya da kuma Manufofin Ci Gaba Mai Ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman burin tabbatar da lafiya mai inganci da bunƙasa masana’antu, ƙirƙire-ƙirƙire da fasaha.

 

Kafin Majalisar ta amince da karatu na biyu, Maigirma Jibrin ya roƙi takwarorinsa da su mara wa kudirin baya. Ya na mai cewa wannan doka za ta kafa tubalin gina tsarin kiwon lafiya na zamani wanda zai kasance mai inganci, haɗin kai, sauƙin amfani da fasaha da kuma amfani ga al’ummomin Nijeriya na yanzu da na gaba.

 

Ya ce, “Wannan kudiri martani ne na doka ga bukatun tsarin kiwon lafiya na ƙarni na 21. Zai samar da tubalin gina tsarin kiwon lafiya na zamani, mai inganci, wanda kowa zai amfana da shi, kuma wanda fasaha za ta kasance ginshiƙinsa. Don haka ina roƙon takwarorina su mara wa wannan kudiri baya domin ya ci gaba da sauran matakan doka.”

 

Kudurin dai ya tsallake karatu na biyu kamar yadda na fada a bisa. Irin wannan kudirori su na fitowa ne kawai daga irin sa da su ka san me duniya take ciki. Lallai Kano ta Arewa da jihar Kano ta yi sa’ar Sanata mai hangen nesa.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Vigilantes Kill Notorious Bandit Leader Kachalla Sani Yellow in Zamfara

Next Post

Wani Mutum Ya Hallaka Matarsa Har Lahira Saboda Ta Ƙi Dafa Abinci

aksam

aksam

RelatedPosts

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi  Annabi Muhammadu SWA  A Garin Nkawkawo
Uncategorized

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

by aksam
September 1, 2026
Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka
Uncategorized

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

by aksam
August 26, 2026
Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano
Uncategorized

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

by aksam
August 26, 2026
Gwajin DNA: Kashi 23.6% Na Gwaje-Gwajen Uba A Najeriya Sun Nuna Rashin Daidaito
Uncategorized

Gwajin DNA: Kashi 23.6% Na Gwaje-Gwajen Uba A Najeriya Sun Nuna Rashin Daidaito

by aksam
August 25, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

‎Kotun Soji A Najeriya Ta Yanke Wa Wani Soja Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

‎Kotun Soji A Najeriya Ta Yanke Wa Wani Soja Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

April 29, 2025

CBN ya musanta cewa ba shi da isassun takardun buga sabon kuɗi

February 11, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media