Daga Hassan Umar Gwammaja
Farashin litar mai ya tashi zuwa Naira 1, 030 daga Naira 897 a gidajen mai na kamfanin NNPC a birnin tarayya Abuja a yau Laraba.
BIZPOINT ta ruwaito Lamarin na baya bayan nan ya faru ne bayan NNPC ya yanke shawarar fita daga yarjejeniyar siyan mai da matatar mai ta Dangote.
Yan Sandan Sun Kama Wani Basarake Da Ake Zargi Da Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Katsina
Hakan na nufin dai, NNPC ba zai ci gaba da zama mai siyan man shi kadai daga Dangote ba.
Premium Times ta rawaito cewa an siyar da man a gidajen man NNPC da safiyar yau kan N1,030 a Abuja.










