Shugaban gwamnatin Jamus Scholz ya buƙaci kasar sa ta bayar da dama ga Yan ci rani inda ya ce babu wata kasa a duniya mai karancin ma’aikata da tattalin arzikinta zai bunkasa.
Shugaban ya baiyana wa majalisar ta Bundestag cewa wannan shi ne gaskiyar lamari kuma dole a fuskanci hakan.
Jawabin nasa na zuwa ne yayin da ake tsakiyar zazzafar muhawara a Berlin kan manufofin cirani da yan gudun hijira.
A ranar talata talata tattaunawa ta ci tura tsakanin kawancen gwamnatin Scholz da ‘yan ra’ayin rikau ba tare da cimma wata matsaya ba.











