Daga: Hassan Umar Gwammaja
Kalaman na Dakta Abdullahi Baffa Bichi, ya zo ne kwanaki kadan bayyan da shi da wasu daga cikin maguya bayansa da kuma sauran wasu jiga jigan ‘yan Jam’iyyar NNPP Suka Sauya Sheka zuwa Jam’iyyar APC a makon Jiya
Aksam Media ta rawaito Baffa Bichi na cewa Shigarsu NNPP ce ta sanya a ka samu nasarar Lashe Zaben Shekara Ta 2023 kuma Hanyar da suka bi suka Samo waccan nasara zasu bi wajen kwace nasarar a zaben Shekara ta 2027
Haka kuma Baffa Bichi ya kara da cewa, Kaddara ce ta hadashi da Kwankwaso amma Dabi’arsu batazo daya ba, dan haka dole mu raba gari dashi acewar Baffa Bichi.
Idan za a tuna dai a watannin baya ne Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauke Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi sakamakon zarginsa na kokarin kawo rarrabuwar kai tsakanin Jam’iyyar NNPP da kuma Gwamnatinsa.









