• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Mutane 25 sun mutu 800 sun jikkata a wata gagarumar fashewa

aksam by aksam
April 27, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
468
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Hukumomi a Iran, sun ce aƙalla mutum 25 ne suka mutu, wasu 800 kuma suka jikkata a wata gagarumar fashewa da ta auku a Daya daga cikin manyan tasoshin jirgen ruwan ƙasar.

Har yanzu ba a tabbatar da abin da ya haddasa fashewar ba a tashar Shahid Rajaee, inda har yanzu wutar ke ci, amma kuma kafofin yada labarai na kasar na nuna yuwuwar hannun Isra’ila a lamarin.

Fashewar wadda ta auku ranar Asabar da safe ta kasance ne a daya daga cikin manyan tashoshin jirgin ruwa na kasuwanci, da ke kusa da birnin Bandar Abbas na kudanci.

Fashewar ta lalata motoci da tagogi da rufin gine-ginen da ke kusa da wajen . Sannan mazauna unguwannin da ke nisan kilomita 30 sun ji kararta.

BBC ta tabbatar da sahihancin wasu hotunan bidiyo da ke nuna wuta na ci ganga-ganga kafin fashewar da da ta auku a wani gidan ajiyar kaya, inda mutane ke gudun tsira da kuma wasu yashe cikin jini a gefen titi kusa da tarkacen da ke cin wuta.

Hoton da aka dauka daga sama ya nuna akalla wuri uku da wutar ke ci inda ministan harkokin cikin gida ya tabbatar da cewa wutar na bazuwa daga sunduki ko kwantaina zuwa kwantaina .

An bayar da umarnin da kada a bude makarantun da ke kusa da wajen a ranar Lahadi.

Wani kamfanin al’amuran da suka shafi tsaro na ruwa ya ce yana ganin kwantainonin da wutar ta tashi suna dauke ne da makamashin da za a hada makamai masu linzami ne da su.

Kamfanin na Ambrey Intelligence ya ce yana ganin wutar ta tashi ne sakamakon rashin alkinta makamashin yadda ya dace.

Kamfanin ya kara da cewa yana sane cewa wani jirgin ruwa na Iran ya sauke wannan makamashi a tashar ruwan a watan Maris da ya gabata.

Ko a can baya daman jaridar Financial Times ta ruwaito cewa wasu jiragen ruwa biyu sun yi dakon makamashi daga China zuwa Iran.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Wata Kotu A Jihar Kano Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Daurin Watanni Biyu Bisa Sare Bishiyu Ba Akan Ka’ida Ba

Next Post

Kaddara Ce Ta Hadani Da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Amma Dabi’ata Batazo Daya Da Tasa Ba:- Dakta Beffa Bichi

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Ƙasashe Biyar da suke bayar da visa kyauta ga yan Najeriya masu passport

Ƙasashe Biyar da suke bayar da visa kyauta ga yan Najeriya masu passport

April 22, 2025
Cikakken bayani kan Dalilan da su ka sanya Ganduje yin murabus a mukaminsa

Cikakken bayani kan Dalilan da su ka sanya Ganduje yin murabus a mukaminsa

June 27, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media