Daga Hassan Umar Gwammaja
Hukumar zabe Mai zaman kanta ta jihar Kano ta sauya lokacin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar zuwa watan oktoba.
Aksam Media ta rawaito Shugaban hukumar faefesa Sani Lawal Malunfashi ne ya sanar da haka yayin Taron masu ruwa da tsaki a Shelkwatar hukumar.
Ya ce sauya lokacin ya biyo bayan bin umarnin kotun koli na tabbatar da ‘yancin gashin Kai ga kananan hukumomin kasar nan daga watan oktoba Mai zuwa.
Faefesa Sani Lawal Malunfashi ya ce hukumar ta Sanya ranar 26 ga watan oktoba na wannan shekara sabanin yadda a baya ta Sanya ranar 30 ga watan Nuwamba Mai zuwa.
Ya ce sauya lokacin gudanar da zaben ya shafi dukkanin lokutan da hukumar ta fitar da suka shafi zaben a baya.











