Daga: Hassan Umar Gwammaja
Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya shaida wa manema labarai cewa sun samu kiran gaggawa daga Garin Kwankwaso Dake ƙaramar Hukumar Madobi, a Jihar Kano inda wani yaro ɗan shekara biyu ya faɗa cikin rijiya.
A wani lamari daban, ya ce jami’an hukumar sun kuma ceto gawar wani matashi mai shekaru 28 da ya faɗa rijiya a garin Kurofawa Yan Kifi da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.
Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da cewa dukkan mutanen biyu sun rasu kafin a samu damar ceto su, duk da gaggawar da jami’an hukumar suka yi wajen kai ɗauki.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin faɗuwar tasu, tare da wayar da kan al’umma kan muhimmancin rufe rijiyoyi da kuma kiyaye lafiyar yara da manya.











