Hukumomin leken asiri daga Nijar, Mali da Burkina Faso sun ce suna shirin bayyana sunayen manyan ’yan siyasan Najeriya da ake zargin suna goyon bayan kungiyoyin ’yan bindiga da ke aiki a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Jami’an tsaron sun bayyana cewa tuni suna da sunayen wasu ’yan siyasa da ake kyautata zaton suna ba wa miyagu tallafi.
Sun ƙara da cewa an riga an kama wasu mutane da ke da hannu wajen samar da makamai ga ’yan bindiga, kuma bincike na ci gaba.
A cewar hukumomin, wannan mataki na cikin ƙoƙarin yankin na rushe hanyoyin laifuffuka na ƙetare iyaka da ke ƙara rashin tsaro a Yammacin Afirka.
Wannan ci gaban ya biyo bayan ƙara haɗin kai tsakanin ƙasashen Sahel wajen sha’anin tsaro, musamman wajen yaƙi da kungiyoyin makamai da kuma safarar haramtattun makamai a tsakanin iyakoki.












