Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jerin ganawa da kusan duk masu faɗa a ji a ƙasar nan a ƙoƙarin sa na janyo hankalin matasa wajen ganin sun jingine shirin su na yin zanga-zanga.
Shugaban ya gana da manyan jami’an gwamnati a ƙoƙarin nemo hanyoyin da za a lallashi matasan su janye ƙudurinsu na yin zanga-zangar.
Misali, sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu sun jagoranci wani taro da ministocin gwamnatin Tinubu a ranar Laraba game da batun.
Haka nan Tinubu ya umarci gwamnoni su koma jihohinsu domin ganawa da mutane tare da lallashin su kan batun zanga-zangar.











