• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

‎Halin Da Venezuela Ta Faɗa Izina Ne Ga Masu Kiran Amurka Ta Kaiwa Najeriya Ɗauki: — MURIC

aksam by aksam
January 6, 2026
Reading Time: 3 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Daga: Hassan Umar Gwammaja

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi, a Najeriya Muslim Rights Concern (MURIC), ta gargaɗi ƴan ƙasar da su guji kiran Amurka ta tsoma baki a harkokin cikin gida, tana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin rikicin makamancin wanda Venezuela ke fuskanta.

Daraktan zartarwa na ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, yana mai kira ga ƴan Nijeriya da su koyi muhimman darussa daga abubuwan da ke faruwa a Venezuela

‎Akintola ya danganta lamarin da rahotannin wani aikin soja da Amurka ta kai a Venezuela, inda aka kama Shugaban ƙasar, Nicolás Maduro, tare da iƙirarin cewa an ɗauki matakai na karɓe iko da arzikin man ƙasar.

A cewarsa, an yi amfani da hujjar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ne a matsayin rufe gaskiyar muradin tattalin arziki, musamman man fetur.

MURIC ta kuma yi watsi da abin da ta kira labarin “kisan Kiristoci” a Nijeriya, tana gargaɗin cewa irin wannan zance na iya zama uzuri na tsoma bakin ƙasashen waje.

‎Ƙungiyar ta ambaci hare-haren tsaro da suka shafi al’ummomin Musulmi a wasu jihohi, tana cewa hakan na ƙaryata iƙirarin wariya ta addini.

‎Farfesa Ishaq ya kuma bukaci ƴan ƙasar da suka zama masu haɗin kai da kuma kare albarkatun ƙasar.

‎A cewarsa, Nijeriya ta tsallake hatsari ne kawai saboda hankalin Amurka ya karkata zuwa Venezuela, wadda ke da manyan rijiyoyin mai fiye da Nijeriya, sai dai ya gargaɗi cewa hakan ba yana nufin Najeriya ta fita daga haɗari gaba ɗaya ba, muddin ake ci gaba da yaɗa labaran da ke neman tsoma bakin ƙasashen waje.

A ƙarshe, MURIC ta yi kira ga shugabanni, malamai da sauran masu faɗa a ji da su yi taka-tsantsan wajen kalamansu, tare da fifita zaman lafiya, fahimtar juna da kare ikon ƙasa.

‎Ƙungiyar ta ce ya zama wajibi ƴan Nijeriya su kalli matsalolinsu a matsayin na cikin gida da za a warware ta hanyar haɗin kai da adalci, ba ta hanyar neman agajin ƙasashen waje ba, domin hakan na iya jefa ƙasar cikin babbar barazana ga tsaro, tattalin arziki da ƴancin kai.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Innalillahi Wa Inna Ilaihirraji’un !!!

Next Post

‎Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Sabbin Dabaru Domin Dakile Satar Amsa A Jarabawar WAEC Da NECO

aksam

aksam

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala
LABARAI

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

by aksam
April 17, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID
Uncategorized

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

by aksam
April 17, 2026
Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka
Uncategorized

Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka

by aksam
April 11, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Invitation !!!

Invitation !!!

August 23, 2025
Yadda direbobin mota ke kokawa da tsadar Man fetur

Yadda direbobin mota ke kokawa da tsadar Man fetur

October 9, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media