• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

‎Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Sabbin Dabaru Domin Dakile Satar Amsa A Jarabawar WAEC Da NECO

aksam by aksam
January 6, 2026
Reading Time: 3 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

Daga: Hassan Umar Gwammaja

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da wasu sabbin dabaru masu tsauri da nufin dakile satar amsa da sauran maguɗan jarabawa a WAEC da NECO, matakan da za su fara aiki daga shekarar 2026.

‎Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Abuja tare da Karamar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmad, inda suka ce an ɗauki matakan ne domin maido da sahihanci, gaskiya da amincewar jama’a ga tsarin ilimi a Najeriya.

‎A cewar wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta fitar, gyare-gyaren sun shafi dukkan matakan gudanar da jarabawar ƙasa, daga shirya tambayoyi zuwa tantance sakamako.

Sanarwar ta ce gwamnati za ta ƙarfafa amfani da fasahohin zamani, tare da tsaurara matakan kulawa, domin rage satar amsa da sauran laifukan da ke lalata martabar jarabawa.

Daga cikin manyan sauye-sauyen da aka sanar akwai sabon tsarin tsara tambayoyi, inda za a rika jujjuya jerin tambayoyi daga ɗalibi zuwa ɗalibi, duk da cewa tambayoyin iri ɗaya ne.

‎Ma’aikatar ta ce wannan dabara za ta rage damar haɗa baki a ɗakunan jarabawa, tare da tabbatar da cewa kowane ɗalibi na rubuta jarabawa ta musamman.

‎Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada haramcin sauya makaranta a matakin SS3, tana mai cewa za a fara aiwatar da dokar cikin kwanaki masu zuwa, domin dakile sauye-sauyen makaranta na ƙarshe da ake zargin suna da alaƙa da satar jarabawa.

A wani mataki na ƙara inganta gaskiya da ɗaukar alhaki, an amince da sabbin ƙa’idojin kimanta ɗalibai na ci gaba (Continuous Assessment), inda aka tanadi lokutan miƙa bayanai kamar haka: Janairu (zango na farko), Afrilu (zango na biyu), da Agusta (zango na uku).

‎Sanarwar ta jaddada cewa dukkan hukumomin jarabawa — ciki har da WAEC, NECO, NBAIS da sauran su — wajibi ne su bi waɗannan ƙa’idoji, domin tabbatar da daidaito da ingancin bayanai a faɗin ƙasar.

Bugu da ƙari, ma’aikatar ta ce za a fara amfani da lambar shaidar ɗalibi ta musamman (Examination Learners’ Identity Number), wadda za ta bai wa gwamnati damar bibiyar ɗalibi a duk tsawon tsarin jarabawa.

‎A cewar jami’an ma’aikatar, wannan mataki zai taimaka wajen ƙarfafa sa ido, inganta tattara bayanai, da samar da ingantaccen tsarin tantancewa na dogon lokaci.

Ɗalibin Da Aka Kama Da Laifin Satar Amsa Za A Haramta Masa Shiga Kowace Jarabawa  Na Tsawon Shekaru Uku — Gwamnatin Tarayya

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

‎Halin Da Venezuela Ta Faɗa Izina Ne Ga Masu Kiran Amurka Ta Kaiwa Najeriya Ɗauki: — MURIC

Next Post

Jirgin Yakin Amurka Sunfurin US Air Force C 130 Ya Sauka A Abuja

aksam

aksam

RelatedPosts

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo
Uncategorized

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo

by aksam
September 5, 2026
Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi  Annabi Muhammadu SWA  A Garin Nkawkawo
Uncategorized

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

by aksam
September 1, 2026
Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka
Uncategorized

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

by aksam
August 26, 2026
Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano
Uncategorized

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

by aksam
August 26, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Ga Sakon Bangajiya Daga:- Ango Isa Sani Abubakar

Ga Sakon Bangajiya Daga:- Ango Isa Sani Abubakar

May 18, 2025
Yadda rundunar yan sanda ta dakume wasu jami’anta da suka yi garkuwa da wani Dan kasuwa

Yadda rundunar yan sanda ta dakume wasu jami’anta da suka yi garkuwa da wani Dan kasuwa

February 6, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media