Daga Khadija Muhammad mai taya
Hukumar zabe mai zaman kan ta jihar kano ta bayyana cewa za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 44 a ranar 30 ga watan Nuwambar na 2024.
Idan za a iya tunawa Aksammedia ta rawaito Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf a kwamakin bayan ya bayyana cewa sun shirya domin gudanar da zaben kananan hukumomin a jihar 44.
Gwamnan ya bayyana hakan ne Kwanaki kadan da kotun kolin kasar nan ta tabbatar da yancin cin gashin kan kananan hukumomi. Kuma ta ce duk karamar hukumar da bata da zababben shugaba ba zata sami kuɗin ta ba .
Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan ga Manema labarai a kano, ranar laraba.










