Wani Sarkin yarbawa ya yi kira ga masu shirin yin zanga-zanga kan tsaɗar rayuwa su yi haƙuri su karawa gwamnatin Bola Tinubu lokaci
Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya ce wahalhalu da tsadar rayuwar da mutane ke kuka a kai, al’amari ne da ya shafi duk duniya
Basarken ya ce duk da haƙƙin ƴan Najeriya ne su yi zanga-zanga amma su kaucewa lalata kadarorin gwamnati domin kansu abin zai dawo
Ooni, Da yake jawabi a shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels, Oba Ogunwusi ya ce:
“Eh tabbas abin da suke nanatawa gaskiya ne, muna shan wahala a kasar nan amma ba a Najeriya kadai ba, al’amari ne na duniya,”
“Ya zama dole mu yi kira (ga masu zanga-zangar) saboda akwai bukatar su ba gwamnatin tarayya ƙarin lokaci kadan domin saita komai tunda abu ne da ya taɓa duniya.”












