Daga Hassan Umar Gwammaja
Gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana fita daga ƙarfe 08:00 na safe a fito a gudanar da harkokin yau da kullum zuwa ƙarfe 02:00 na rana.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Baba Halilu Ɗan Tiye, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Aksam Media Kano, a daren Asabar 03 ga watan Yulin 2024, ya ce an sassauta dokar ne domin al’umma su fito su gudanar da harkokin su na yau da kullum, bisa damuwar da aka shiga.
Ya ci gaba da cewa, yanzu mutane suna da damar da zasu fito su gudanar da al’amuran su kamar yadda aka saba a baya, yana mai cewa gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya damu matuƙar gaske kan yadda al’ummar jihar suka samu kan su a ciki.
Majiyar Aksam Media Kano, ta rawaito cewa, hakan na zuwa ne bayan da wasu matasa suka shirya gudanar da zanga-zangar lumana akan tsadar rayuwar da aka samu kai a ciki, domin sanar da gwamnatin tarayya halin da suke ciki dan ɗaukar mataki.











