• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Gwamna Abba Na Shirin Naɗa Murtala Garo A Matsayin Mataimaki:— Rahotanni

aksam by aksam
April 1, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home SIYASA
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga; Hassan Umar Gwammaja

RelatedPosts

Daukar DanKwankwaso Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano A NDC Ya Jaho Ce-ce-ku-ce

An Kona Fastocin Peter Obi Da Kwankwaso A Jihar Kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Koma Jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) A Hukumance; Inda Ya Karɓi Katin Zama Mamba Na Jam’iyyar

Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na ci gaba da tattara bayanai da shawarwari domin tabbatar da yiwuwar naɗa Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakinsa.

Majiyoyin sun ce gwamnan na gab da kammala tattaunawa da muhimman masu ruwa da tsaki, musamman daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), domin cimma matsaya kan wannan mataki.

A baya-bayan nan dai an samu ɗan tangarda tsakanin wasu ƙusoshin siyasa da gwamnan ya tarar, lamarin da ya haifar da saɓani kan batun wanda zai maye gurbin mataimakin gwamna. Sai dai rahotanni sun nuna cewa, bayan jerin ganawa a ɓoye da aka gudanar a lokuta daban-daban, an samu daidaito tare da rage duk wata barazana ta rikici.

Wata majiya mai kusanci da gidan gwamnati, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida cewa gwamnan ya gudanar da muhimman ganawa da jagororin siyasar Kano ta Kudu, inda ya samu goyon bayansu kan zaɓin Garo domin riƙe mukamin mataimakin gwamna.

Hakazalika, an rawaito cewa wasu daga cikin jiga-jigan siyasa da ke ƙarƙashin tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, sun nuna amincewa da wannan zaɓi, duk da cewa akwai wasu ‘yan tsiraru da ke nuna adawa bisa dalilai na siyasa.

Murtala Sule Garo, wanda ya taɓa zama kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar, shi ne kuma tsohon ɗan takarar mataimakin gwamna na APC a zaɓen 2023. Yanzu haka ana ganin yana da ƙarfi wajen karɓar wannan muƙami, bayan murabus ɗin da tsohon mataimakin gwamnan, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi a ƙarshen makon da ya gabata.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da wannan batu.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

HAJJIN 2026: Irin Halin Da Sama Da Maniyyata 1,000 Suke Ciki A Jihar Kaduna

Next Post

Donal Trump Ya Sanya Wa’adi Dakatar Da Yaki Da Iran Ko Da Babu Yarjejeniya

aksam

aksam

RelatedPosts

Daukar DanKwankwaso Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano A NDC Ya Jaho Ce-ce-ku-ce
SIYASA

Daukar DanKwankwaso Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano A NDC Ya Jaho Ce-ce-ku-ce

by aksam
June 16, 2026
An Kona Fastocin Peter Obi  Da  Kwankwaso  A Jihar Kano
SIYASA

An Kona Fastocin Peter Obi Da Kwankwaso A Jihar Kano

by aksam
June 1, 2026
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Koma  Jam’iyyar National Democratic Congress (NDC)  A Hukumance; Inda Ya Karɓi Katin Zama Mamba Na Jam’iyyar
SIYASA

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Koma Jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) A Hukumance; Inda Ya Karɓi Katin Zama Mamba Na Jam’iyyar

by aksam
May 3, 2026
Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Umarci  Duk Masu Riƙe Da Mukaman Siyasa Dake Da Niyyar Tsayawa Takara Dasu Yi Murabus Kafin Ranar Juma’a 24 ga Watan Afrilu 2026
SIYASA

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Ya Fice Daga Jam’iyar PDP

by aksam
May 2, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Appreciation Message 

Appreciation Message 

February 11, 2026
Yadda wani gwamna ya yi koyi da Gwamnan jinar kano Abba Kabir Yusuf

Yadda wani gwamna ya yi koyi da Gwamnan jinar kano Abba Kabir Yusuf

January 29, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media