Daga Abubakar Sadeeq
Bayan yaɗuwar hotuna da bidiyon wani katafaren gida da ake rushewa a Unguwar Rijiyar Lemo, tare da iƙirarin cewa an sayar da shi mako guda bayan rasuwar mai gidan, bincike ya gano cewa labarin ba haka yake ba.
Gidan da ake magana a kai yana daga cikin tsofaffin kuma fitattun gidaje a Unguwar Rijiyar Lemo. Ana danganta shi da *Alhaji Muhammad (Sakwaya)* ne saboda shi ne ya gina gidan tun kimanin shekaru 30 da suka gabata, kusan a shekarar 1998, kuma ya shahara a unguwar. Sai dai *Alhaji Muhammad (Sakwaya) yana nan da ransa cikin ƙoshin lafiya, kuma ya riga ya rabu da gidan tun shekaru da dama da suka gabata*, don haka ba shi ne ya sayar da gidan a wannan karon ba.
Bayan hotuna da bidiyon rushewar gidan sun fara yawo a TikTok, WhatsApp, Facebook, X da sauran shafukan sada zumunta, wasu suka fara yaɗa cewa an sayar da gidan ne mako guda bayan rasuwar mai gidan, tare da iƙirarin cewa an sayar da shi kan kuɗi har biliyoyin naira.
Sai dai majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa wannan ba gaskiya ba ne. A cewarsu, *mai gidan na baya* ya riga ya sayar da gidan tun watanni kafin rasuwarsa, an kuma kammala biyan kuɗin cinikin gaba ɗaya. Bayan haka, an ba shi sanarwar ya fice daga gidan, sai dai Allah Ya ƙaddara ya rasu kafin lokacin da zai bar gidan.
Majiyar ta kuma ƙaryata rahotannin da ke cewa an sayar da gidan kan *Naira biliyan 2*, *biliyan 1* ko *miliyan 200*, tana mai cewa waɗannan adadi jita-jita ne, ba tare da bayyana ainihin kuɗin cinikin ba.
Dangane da rushewar gidan kuwa, sabon mamallakin ya bayyana cewa tun farko ba niyyarsa ba ce ya ci gaba da amfani da ginin. Ya ce yana shirin rushe gidan ne domin gina shagunan kasuwanci, kasancewar filin na maƙotaka da *Kasuwar ‘Yan Hula ta ‘Yan Moji*, da ke Layin Makarantar Allo a Unguwar Rijiyar Lemo.
Binciken ya nuna cewa labarin da ake yaɗawa na cewa an sayar da gidan mako guda bayan rasuwar mai gidan ba daidai ba ne. Gaskiyar magana ita ce *an riga an kammala cinikin gidan tun kafin rasuwar wanda ke zaune a cikinsa, yayin da rushewar ginin kuma wani ɓangare ne na shirin sabon mamallakin filin.*










