Aƙalla gwamnoni shida sun yi alƙawarin ɗaukar darussa masu amfani daga Yankin Masana’antu na Glo-Djigbé (GDIZ) da ke Jamhuriyar Benin domin farfaɗo da masana’antar yadi a Najeriya.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne yayin da suka raka Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wajen duba wannan haɗaɗɗen yankin masana’antu da ke kusa da birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ziyarar na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kafa cibiyoyin sarrafa kayayyakin amfanin gona da bunƙasa masana’antun cikin gida a faɗin ƙasar.
Tawagar ta haɗa da Gwamna Hope Uzodimma na Jihar Imo, Gwamna Dauda Lawal na Zamfara, Gwamna Caleb Mutfwang na Plateau, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, Gwamna Dikko Radda na Katsina da kuma Gwamna Umar Namadi na Jigawa.
Gwamnonin sun bayyana cewa tsarin GDIZ ya nuna yadda ingantattun manufofin gwamnati, ingantattun ababen more rayuwa da jarin kamfanoni masu zaman kansu za su iya haɗa manoma da masana’antun sarrafa kayayyaki, rage fitar da albarkatun ƙasa ba tare da an sarrafa su ba, tare da samar da ayyukan yi a fannonin noma da masana’antu.










