• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Fassarar kalaman shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na zagayowar yancin kai

aksam by aksam
October 1, 2024
Reading Time: 3 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
468
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Hassan Umar Gwammaja

A ranar talatar 10/10 kasar nan ta cika shekaru 64 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka na burtaniya.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

A duk irin wannan rana ta 10/10 shugaban ƙasa ya kan fito ya yi jawabi ga al’ummar kasa, Sannan ya bayyana nasarorin da ya samu da kuma taya su Yan kasar murnar zagayowar wannan rana.

Kamar kowacce shekara a yau ma shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya gabatar da jawabin ga yan Nigeria kamar yadda aka sanar tun ajiya

Fannin tsaro:
Jawabin shugaban ƙasar ya tabo matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar musamman Arewa maso gabas da arewa maso yamma, Inda ya ce gwamnatinsa tana ita bakin kokarinsu ta wajen magance matsalolin don tabbatar da zaman lafiya ga yan Nigeria.

Ya ce a cikin shekara guda gwamnatinsa ta kawar da kwamandojin Boko Haram sama da 300 tare da hallaka shugabannin yan fashin daji masu tari yawa wadanda suka addabi al’umma.

Ya ce sojojin ƙasar suna aiki ba dare ba rana domin kawar da duk wani nau’i na ta’addanci a cikin al’umma.

Tattalin arziki:

Abu na biyu shi ne ya ce gwamnatinsa tana iya bakin kokarinta wajen inganta tattalin arzikin Nigeria daga mawuyacin halin da yake ciki.

Ya ce ya fito da manufofin sauya fasalin tattalin arzikin kasa wanda ya jawo al’umma suke kokawa da shi, amma dai ya ce hakan ba ba dan lokaci ne domin zuwa yanzu an fara ganin cigaba Kan aiyukan garanbawul din da ake yiwa tattalin arzikin.

Ya ce yanzu haka saboda ci gaban tattalin arzikin da ake samu masu zuba jari daga kasashen waje a shekara guda sun zuba jarin Dala biliyan $30 a fadin Nigeriya.

” Tsarin da babban bankin Nigeria CBN ya dauka na kiyaye manufofin Kudade ya tabbatar da tsaro da tabbas a kasuwar chanjin kudaden waje.

Ya ce ya gaji Dala biliyan 33 a asusun ajiyar Nigeria na kasashen waje, sannan sun biya bashin dala biliyan 7 da biyan sauran basussuka da ake bin Nigeriya kamar yadda suka yi alkawari.

Ya ce duk a kokarinsa na ganin an inganta walwalar Nigeriya ne tasa gwamnatinsa ta dawo da yancin cin gashin kan kananan hukumomi a Nigeriya ta fuskar kudade.

Tsadar kayan Abinchi:

Ya ce yasan ana fama da matsalolin tsadar kayan abinchi, amma ya ce ba a Nigeriya ne kadai aka fuskantar wannan matsala ba , amma ya ce gwamnatinsa tana iya bakin kokarinta domin wadata kasar da Abinchi.

Ya ce gwamnatinsa tana bunkasa harkokin Noma ta hanyar bada tallafi ga manoma da samar da takin zamani ga manoma don su sami sauki wajen gudanar da aikin nasu na noma don wadata kasar da Abinchi.

Ya ce sun samar da ma’aikatar kera kayan noma na zamani wadanda zasu taimakawa manoman wajen barin tsahon tsarin noma zuwa sabon tsarin noma wanda zai taimakawa ƙasar.

Tsadar Mai da sufuri :

Game da batun sufuri, shugaban Bola Tinubu ya ce suna daukar matakan da suka dace domin saukaka al’amuran sufuri a tarayyar Nigeria.

Ya ce a kokarin hakan ne suka fara bayar da da motoci masu amfani da Iskar Gas da masu amfani da lantarki ga kungiyoyin Kwadago da na dalibai domin saukaka ma’aikata da dalibai a Nigeriya.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta taimakawa gwamnonin jihohin Nigeria don su sayi motocin masu amfani da Iskar Gas don saukakawa al’ummarsu harkokin sufuri.

Matasa:
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta fito da damamaki masu yawa ga matasa domin tallafa musu kasancewar sune kashin bayan cigaba kowacce al’umma.

Ya kuma sanar da cewa za a gudanar da wani gagarumin taron matasa na kasa wanda zai kunshi dukkanin matasa daga bangarorin kasar nan, kuma yace taron zai baiwa matasa bayyana Kalubalensu da kuma hanyoyin da za a magance su, Sannan ya bayar da tabbas gwamnatinsa zata aiwatar da shawarwarin da aka bata bayan taron.

Sanna ya yi alkawarin cigaba da baiwa matasa damar shiga harkokin gwamnatinsa ta yadda matasan zasu fahimci abubunwan da Ake yi a gwamnati ko dan gobe.

Sannan ya yi alkawarin gwamnatinsa ta karkashin ma’aikatar Kwadago da samar da aiyukan yi, za ta samar da aiyukan yi ga matasa miliyan biyu da rabi a kowacce shekara don rage adadin matasan da ke zaman kashe wando.

Hadin kai
Shugaban ƙasar Nigeriya Bola Ahmad Tinubu ya kuma bukaci al’ummar kasar da su zamo masu haɗin kai, inda yace da shi ne kasar zata kai duk Inda Ake bata.

Ya bukaci kowa ya ajiye bambancin kabila ko addini ya bayar da gudunmawa wajen ciyar da ƙasar gaba don yan baya su amfani kasar kamar yadda gwamnatinsa take fata.

Daga ƙarshe dai ya yabawa Yan ƙasar bisa juriyar da suke nunawa a wannan lokaci mai matukar kalubale, inda ya bada tabbatacin nan gaba kadan komai zai daidaita.

.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Babu abin da zai hana mu fita zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoban 2024: Dan takarar shugaban kasa

Next Post

Rahoto kan yadda Angulu ke neman karewa a wasu sassan Duniya

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Mutane takwas sun rasa rayukansu bakwai na asibiti sanadiyar rushewar bene mai hawa daya

Mutane takwas sun rasa rayukansu bakwai na asibiti sanadiyar rushewar bene mai hawa daya

June 29, 2024
Kasar Senegal Ta Lashe Gasar AFCON Bayan Doke Mai Masaukin Baƙi

Kasar Senegal Ta Lashe Gasar AFCON Bayan Doke Mai Masaukin Baƙi

January 18, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media