Kasar Sin ta gabatar da abin da ake kira dashen ƙashi na farko a duniya da aka ƙera daga sabon sinadarin titanium da tagulla, lamarin da ke nuna wani babban ci gaba a fannin fasahar likitanci da kirkire-kirkiren tiyata.
An samar da wannan sabon dashen ne bayan fiye da shekaru 10 ana gudanar da bincike da gwaje-gwaje. Sabon sinadarin ya haɗa titanium da tagulla domin samar da abu mai matuƙar ƙarfi, ɗorewa da juriya. Masana sun bayyana cewa wannan kirkira za ta taimaka wajen inganta dashen ƙashi da ake amfani da shi wajen tiyatar ƙashi da gyaran karaya.
Ɗaya daga cikin manyan fa’idodin sabon sinadarin shi ne rage haɗarin kamuwa da cututtuka bayan tiyata, wanda ke daga cikin manyan ƙalubalen da ake fuskanta a tiyatar ƙashi. Masu bincike sun ce sinadarin tagulla na da kaddarorin kashe ƙwayoyin cuta, wanda zai taimaka wajen sa marasa lafiya su warke cikin sauri tare da rage matsalolin da ka iya tasowa bayan tiyata.
Hukumar Kula da Kayayyakin Magunguna ta Ƙasa ta kasar Sin ta amince da amfani da ƙusa ta farko da aka ƙera daga sabon sinadarin titanium da tagulla domin amfani a asibitoci. Wannan mataki zai buɗe hanya ga faɗaɗa amfani da wannan fasaha a cibiyoyin lafiya da asibitoci a faɗin ƙasar.










