Daga cikin dalibai 1,969,313 da suka rubuta jarabawar a makarantu 23,554, Dlibai 754,545 ne suka samu akalla credits guda biyar ciki har da Turanci da Lissafi — wato kashi 38.32% — . Wannan na nuna raguwar kashi 33.8% idan aka kwatanta da kashi 72.12% da aka samu a shekarar 2024.
A yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar WAEC dake Yaba, Legas, ranar Litinin 4 ga Agusta 2025, shugaban ofishin WAEC na kasa, Dr. Amos Dangut, ya danganta wannan koma baya da sabon tsarin da WAEC ta bullo da shi na nuna bambancin takardun jarrabawar objective a muhimman darussa kamar Turanci, Lissafi, Biology da Economics.
“Wannan tsari ya rage yawaitar hadin baki da aikata magudi a jarabawa. Mun lura da raguwar sakamako a bangaren objective, amma sakamakon essay bai canza sosai ba. Wannan wani karfi ne na nuna cewa dalibai su maida hankali wajen shiri da kansu,” in ji Dangut.
An gudanar da jarrabawar daga 24 ga Afrilu zuwa 20 ga Yuni, 2025, yayin da aikin duba sakamako ya gudana daga 3 zuwa 21 ga Yuli. WAEC ta kuma yi amfani da sabon tsarin lissafi na zamani kai tsaye domin hanzarta fitar da sakamako cikin lokaci.
Daga cikin yawan daliban da suka rubuta, 1,517,517 (wato kashi 77.06%) sun samu sakamakon su cikin koshin lafiya, yayin da sakamakon 451,796 (kashi 22.94%) ke kan aiki saboda matsalolin fasaha. WAEC ta tabbatar da cewa za a warware matsalolin cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Game da magudin jarrabawa, 192,089 daga cikin sakamakon — wato kashi 9.75% — an dakatar da su saboda laifuffuka irin su amfani da wayoyin hannu da aka haramta da kuma hadin baki. Wannan adadin bashida yawa idan aka kwatanta da kashi 11.92% da aka dakatar a 2024.
“Wadanda ke aikata wadannan laifuka suna zama kalubale a gare mu. Wasu ma har suna amfani da sunan WAEC suna yada labaran bogi. Mun kama wasu, kuma hukunci ya wajaba a kansu,” in ji Dangut.
Dangut ya kuma ce jihohin da ake bin su bashi ba za su iya samun sakamakon daliban da suka dauki nauyin su ba har sai sun biya bashi.
A bangaren daliban da ke da bukatu na musamman, 12,178 ne suka yi rajista. Daga ciki, 112 na fama da rashin gani, 615 na da matsalar kunne, 52 na da matsalolin kwakwalwa, sai kuma 37 masu nakasa ta jiki. WAEC ta tabbatar da cewa an ba su dukkanin kulawa ta musamman da ake bukata.
Dangane da jinsin dalibai, 976,787 (wato kashi 49.60%) maza ne, yayin da 992,526 (kashi 50.40%) mata ne.
Daga cikin 754,545 da suka samu credits guda biyar da suka hada da Turanci da Lissafi, mata sun fi maza da kashi 53.99% (407,353), yayin da maza suka kasance kashi 46.01% (347,192).
An fitar da sakamakon ne a hukumance ranar Litinin ta shafin WAEC na X (Twitter). Inda aka umarci Dalibai da su ziyarci http://waecdirect.org domin ganin sakamako.












