Jami’an tsaron gidan yarin sun ce sun tare magen ne a ranar 21 ga watan Yuli, bayan sun gano tana ɗauke da wasu ƙananan kunshe-kunshen miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye cikin wata kwala da aka saƙa da hannu aka ɗaura mata a wuya.
ICPC Ta Gano Ma’aikatan Bogi 908 A Wasu Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya 50
Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa abubuwan da aka maƙala wa dabbar miyagun ƙwayoyi ne, lamarin da ya sa jami’an suka ƙwace su nan take domin ci gaba da bincike.
Bayan an tabbatar da lafiyar magen, hukumomin suka sake ta, yayin da suke ci gaba da neman mutanen da suka shirya amfani da ita wajen shigar da haramtattun ƙwayoyi cikin gidan yarin.
Lamarin ya jawo hankalin jama’a, domin ya nuna yadda masu aikata laifuka ke ƙirƙiro sabbin dabaru na kauce wa matakan tsaro wajen safarar haramtattun kayayyaki.









