Daga Hassan Umar Gwammaja
A ranar Lahadi data gabatane al’ummar Garin Zangon Nkawkawo Dake Kasar Ghana suka gudanar da taron Walimar Saukar Karatun Al’qur’ani Mai Girma gamin da Addu’o’in samun zaman lafiya tare da yi wa sauran ‘yan asalin garin da suke zaune kasashin waje fatan alkairi da kuma yi mu su murnar shegowar sabowar shekarar musulunchi ta 1448 bayan hijjira
An gudanar da taro ne a Babban Masallachin Juma’a na Garin Nkawkawo, Karƙashin Jagoranci Mai Martaba SARKIN ZANGO NKAWKAWO Alhaji Abdul-nasir Usman da Sauran Sarakunan kabilu mazauna garin tare da Majalisar Malamin Karƙashin Babban Limamin Garin Sheikh Nura Adam
In da aka yi Saukar Karatun Al’qur’ani har su goma sha daya tare da karanta littafin jala’ilu kairati sai uku
Taron yasa mu halartar ‘yan siyasa da shugabanin al’umma irin su MC na kwahu a majisar kasa Hon. Tanimu Haliru da sauransu.









