Hukumar kwalejin Aminu Kano College of Education (AKCOE) kwalejin al’umma na godiya ga Allah subhanahu wa ta’ala bisa ga gagarumar nasarar da ta samu na yaye daliban digiri na farko tare da ci gaba da gudanar da karatun degree bisa cikakken hadin gwiwa da Jami”ar tarayya ta Dutsin ma wato federal university Dutsin ma.
Kaman yadda aka sani, Wannan kwalejin ta AKCOE tana gudanar da digri akan fannoni daban daban bisa tsarin FULL TIME DA PART TIME daga litinin har zuwa lahadi daidai da buqatar dalibi.
Karin tagomashi, Federal University Dutsin-Ma ta sake bada dama r yin karatun BABBAR DIPLOMAR gaba da digiri wato PGDE wanda dalibi zai yi karatun ta harshen turanci ko larabci duk a wannan kwalejin.
Ga masu bukatar yin digiri a fannoni daban daban, kamar yadda aka sani manyan Profesoshi da Daktocin ilimi nanan a shirye domin bada ingantaccen ilimi.
Baya ga soke santocin da FUDMA tayi, wanda bai shafi Aminu Kano College of Education (AKCOE) ba, domin ita hadin gwiwace kai tsaye da FUDMA (wato Affiliation).
Muradin Kwalejin Aminu Kano College of Education (AKCOE) kwalejin Al’umma shine samar da ingantaccen ilimi akan farashi mai sauki domin gina Al’umma.










