Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta ce ta kayade farashin kudin shinkafa a kasuwanin kasar.
Gwamantin tace bayan dogon bincike da ta gudanar tsakanin masu ruwa da tsaki ta tsayar da farashin duba da yadda ba inda ake sayar da shinkafa sama da CFA Jika 13.
Cikin wata sanarwa da ministan harkokin kasuwanci na kasar ya sanya wa hannu, ya gwamnatin kasar ta dauki matakin karyar da farashin shinkafar da ake shigar da ita cikin kasar.
Sanarwar ta kuma kayyade sabon farashin da za a rika sayar da shinkafar a fadin kasar, daga jaka 16 da rabi ko 17, zuwa jaka 13 da rabi ko 14 a wasu jihohin kasar,












