Dan gwagwarmayar kungiyar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho, ya komo Najeriya shekaru biyu bayan ya yi gudun hijira zuwa Jamhuriyar Benin.
Ya komo Najeriya ne domin binne mahaifiyarsa, wadda ta rasu a lokacin da yake tsare kuma ya ke fuskantar shari’a a Jamhuriyar Benin.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki, ya fitar a shafin X a ranar Alhamis, 22 ga Fabrairu, ta tabbatar da cewa dan gwagwarmayar ya dawo kasar.
Zan iya tabbatar da cewa Cif Sunday Adeyemo yana kan hanyarsa ta zuwa garin Igboho domin yin jana’izar mahaifiyarsa Misis S.A Adeyomo.”
Har ila yau, Koiki ya wallafa wani faifan bidiyo wanda aka gano Igboho tare da wasu mutane da ake kyautata zaton suna wurin daukar gawar mahaifiyar ne.











