Ƙungiyar likitoci ta ƙasa, Nigerian Medical Association (NMA), ta dakatar da Shugabanta na Ƙasa, Farfesa Bala Audu, bisa zargin take dokokin kundin tsarin mulki da kuma nuna halin kama-karya.
An cimma wannan mataki ne a ranar Laraba yayin wani taron gaggawa na wakilai (Emergency Delegates Meeting – EDM) da aka gudanar a Abuja, inda wakilai 63 suka halarta, ciki har da shugabanni da sakatarori daga jihohi 23 da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT).
Ana zargin Audu, wanda shi ne shugaban Kwamitin Manyan Jami’an ƙungiyar (National Officers Committee – NOC), da dakatar da ‘yan takara shida ba tare da tuntuba ba daga shiga zaɓen ƙasa mai zuwa, wanda za a gudanar a yayin Babban Taron Shekara-shekara na NMA (AGM) a Kano daga ranar 27 ga Afrilu zuwa 3 ga Mayu.












