Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara a kotun koli yana kalubalantar tsige shi da kotun daukaka kara ta yi a makon jiya.
Kadaura24 ta ruwaito cewa Abba Kabir Yusuf ya shigar da karar ne a yau Laraba.
A cikin sanarwar daukaka karar da jaridar kadaura24 ta gani, jam’iyyar Abba Kabir Yusuf ta NNPP ta shigar da karar, jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Takardar wadda ta bayyana dalilai 10 na daukaka kara kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, ta bukaci kotun koli ta duba hukuncin.
Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne kotun daukaka kara ta soke zaben gwamna Yusuf inda ta bayyana cewa rashin sanya sunansa a rajistar jam’iyyarsa da INEC ta yi ya saba wa sashi na 177 (c) na kundin tsarin mulkin 1999, wanda ya bukaci kowanne dan takarar ya zama yana da jam’iyya kafin tsayawa takara.
Hukuncin ya sabawa ra’ayin karamar kotun sauraron kararrakin zabe, wadda ta ce kotun ba ta da hurumin tantance ‘yan jam’iyya.
Kotun daukaka kara ta kori gwamnan tare da bayyana abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna na APC a matsayin zababben gwamnan jihar Kano.












