• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Ya kamata Direbobin Manyan motoci, su daina gudu wuce sa’a, cewar shugaban kungiyar su.

aksam by aksam
November 22, 2023
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Kungiyar matuka manyan motocin haya dake kasuwar Tafawa Balewa ta bukaci direbobin manya motoci na unguwar Tafawa Balewa da su kasance masu bin dokokin hanya,Musamman su da suke bin manyan hanyoyin kudu da Arewacin Kasar nan.

Shugaban Sashin Kula da harkokin Sufuri na Kungiyar Alhaji Halliru Ibrahim Gizina ne,ya bukaci hakan a Lokacin da yake zantawa manema labarai a ofishinsa dake Tafawa Balewa anan jihar Kano.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Halliru Ibrahim Gizina yace,ba wai sai lokacin hunturu ba za,a ja hankalin Direbobi ba,kan su rika kiyayewa da umarnin Hukumomi masu kula hanyoyi da kaucewa gudun ganganci ba,inda yace,Shugaban A A Gizina, ya himmatu wajen ganin an inganta harkokin tuki da hakkokin direbobin dake safara zuwa jihohin Kudu da Arewacin Najeriya.

Halliru Gizina, yayi kira ga matuka manyan motoci su tabbatar suna bin dokoki da kaidoji yadda suka kamata domin kaucewa afkuwar haddura.

Yace,kamata yayi direbobi su zamto masu bin dukkannin dokokin da aka gindaya musu domin samun nasarar da aka sanya a gaba na ciyar da harkokin Sufurin Manyan motoci ta yadda jihar Kano za ta yi gogayya da sauran jihohin kasar nan.

Haka zalika,ya bayyana cewa, wannan lokaci ne daya kamata duk wani direba ya kasance masu kulawa a lokuta daban daban, ba ma sai an Shawarce su ba,su kiyaye dokokin da aka sanya akan al’amuran da suka shafi tuki.

Halliru Gizina ya yabawa Gwamnatoci a matakai daban daban da Hukumomin dake lura da harkokin Tuki bisa jajircewa da suke yi wajen wayar da kan direbobi domin ciyar da al’amuran da suka shafi Sufuri.

Yace, Kungiyar Direbobin Manyan motoci ta Tafawa Balewa za ta ci gaba da baiwa Gwamnatoci da hukumimin cikakken hadin yadda ya kamata domin bunkasar harkokin Sufuri a jihar Kano da ma kasa baki daya.

Ibrahim sani gama pyramid radio

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Shari’ar zabe, gwamnan Kano ya garzaya kotun koli

Next Post

Nasarar Da Gwamna Uba Sani Ya Samu a Kotun Daukaka Kara Dake Abuja Ta Al’ummar Jihar Kaduna ce:- Yusuf Umar Kirgi

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Innalilahi Wa’inna ilahi Rajiun !!!

Innalilahi Wa’inna ilahi Rajiun !!!

April 12, 2024
Bitadakullin siyasa, an yi gidan kaso da sakataren jam’iyar PDP

Bitadakullin siyasa, an yi gidan kaso da sakataren jam’iyar PDP

February 14, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media